Da Dumi-Dumi ! muna kira ga Buhari ya tsige Ministan Shari’q Abubakar malami San – Isah Sadiq Achida
Shugaban jam’iyyar APC a jihar Sokoto Hon. Isah Sadiq Achida ya zargi Ministan Shari’a na kasa kuma jigo a jam’iyyar APC Abubakar Malami da aiki da PDP ta karkashin kasa domin kawo ma jam’iyyar APC nakasu a babban zaben 2023 da ke tafe.

Achida ya ce Malami yana wannan aiki ne ta hanyar kawo wasu da ya ke yi ganin za su taimaka masa wajen rusa jam’iyyar a zaben 2023.
“Baya ga wannan, Abubakar Malami ya taka dokar Shari’a, domin ya bayyana sakamakon Shari’ar da ke gudana a jam’iyyar APC a jihar Sokoto tsakanin bangaren Sanata Wamakko da Abdullahi Balarabe Salame, inda ya zabi bangaren da yake ra’ayi tare da bayyana su a zaman wadanda su ka samu nasara, dudda kasancewar wannan shari’a tana gaban Alkali. Wanda hakan ya nuna cewa bai san abin da yake yi ba, bai dace da matsayin da yake kan shi ba”.
Achida ya ci gaba da cewa” Akwai wasu ya’yan jam’iyyar APC a jihar Sokoto wadanda kowa ya sani cewa yaran Gwamna Tambuwal ne na jam’iyyar PDP, amman dudda haka Abubakar Malami ya zabi kulla alaka da su fiye da halattattun ya’yan jam’iyyar wadanda su ka wahala da ita a zaben 2019. Kuma kowa ya sani cewa babban aminin Gwamna Tambuwal ne, yana kullawa jam’iyyar zagon kasa ne daga karshe idan ta ruguje ya bar ta”.
“Akwai bukatar uwar jam’iyyar ta kasa ta san xa wannan zagon kasa da Abubakar Malami ya ke yi wa jam’iyyar tun da wuri, matukar shugabannin wannan jam’iyya na son ci gaban ta da kuma dorewar ta kan karagar mulki”.
“Kowa ya sani cewa wadannan mutane da ya kulla alaka da su domin rugaza jam’iyyar APC a cikin su babu wanda zai iya kawo karamar hukuma guda daya tak a jihar sa. Shine sai ya yi amfani da su domin cikar burin sa na rugaza jam’iyyar APC cikin sauki”.Inji shi.
“Daga karshe mu na kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kore shi tunda har zai iya yi wa jam’iyyar da ta masa riga da wando zagon kasa”
(Nasara)




