Tsige Buhari za mu yi tunda dai shi ba Allah bane – Hon.Jagaba Adams
Rahotanni sun nuna cewa wani dan majalisar wakilai, Jagaba Adams Jagaba ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A cewar dan majalisar, babu wani abu da ake fuskanta a wannan mulkin baya ga bakar wahala da matsananciyar yunwa.
Jagaba ya kasance dan majalisa mai wakilatar Kachia da Kagarko na jihar Kaduna.
Furucin dan majalisar na zuwa ne bayan da majalisar dokokin kasar tayi barazanar tsige shugaba Buhari idan har bai aiwatar da kudurorin da suka zartar ba.
Mista Jagaba ya ce idan har Shugaba Buhari bai aiwatar da kudurorin da suka bukata ba to za su tsige shi a bisa tsarin kundin mulkin kasa.
Jagaba ya jadadda cewa basa dari-dari akan yiwuwar hakan saboda
“Buharin ba Allah ba ne kuma bai yi kama da Annabi ba, duk inda ya yi kuskure za mu take shi” .
Sources:mikiya