Labarai
Da duminsa: Matasa sun kone gidan iyayen Gwamnan Legas, Sanwo-Olu (Bidiyo)
Advertisment
Bayan wani lokaci, matasan sun yi nasarar kone gidan kurmus.
Ganau din wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce, “Wurin karfe 7:45 na safe, fusatattun matasa sun taru wurin gidan iyaye Sanwo-Olu da ke kan titin Omididun a Lagos Island inda suka dinga jifa tare da fasa gilasai. “Daya daga cikin matasan ya zuba fetur inda aka hana shi saka wuta saboda tsoron rasa rayuka. “Amma kuma daga bisani matasan sun taru inda suka kone gidan.
A halin yanzu ‘yan hukumar kwana-kwana ne ke kashe wutar.” An gano cewa ‘yan sandan da ke yankin Adeniji Adele ne suka gaggauta zuwa wurin gobarar domin kwantar da tarzoma.
Ga bidiyon nan kasa.