Kannywood

Tabarakallah: Bilkisu Shema ta kai ziyara Ga masoyinya har wajen sana’arsa (hotuna)

Advertisment

Tabarakallah: Bilkisu Shema ta kai ziyara Ga masoyinya har wajen sana'arsa (hotuna)
Kwatsam jiya Asabar da misalin 11:00 na dare sai ga mota ta tsaya, a gurin da ake sayar da Shayi a bakin Sabuwar Babbar Tashar Jahar Katsina, sai ga Mota kirar 406 da Bakin Gilashi.
Idanuwan Mutanen da ke zaune a gurin suka koma gurin don ganin wanda zai fito daga Motar, bude Kofar ke da wuya sai ga Jarumar Finafinan Hausa Bilkisu Shema fitowarta ke da wuya aka fara kuwwa da ihu, da mamakin yadda ta cika alkawarin ziyartar wannan bawan Allah, Kamar yadda ta shedawa Abokin aikinta Hassan Danja.Tabarakallah: Bilkisu Shema ta kai ziyara Ga masoyinya har wajen sana'arsa (hotuna)
Shi dai wannan bawan Allah mai suna Buhari Bross kamar yadda kowa ua sani, a kowane lokaci labarinshi bai wuce Bilkisu Shema, ya sha fadawa Mutane cewa shi Masoyinta kuma dan gani kasheninta, ya kaf cikin Jaruman Finafinan Hausa babu kamar Bilkisu Shema.
Gwanin birgewa da ban sha’awa ta fito har inda yake sana’ar ta tsaya, bayan ta gaida Mutanen da ke gurin suka gaisa da masoyin nata har suka dauki hutuna, tsawon mintuna biyar ana gaisawa tare da mai da magana daga karshe ta karbi lambarsa suka yi bankwana.Tabarakallah: Bilkisu Shema ta kai ziyara Ga masoyinya har wajen sana'arsa (hotuna)
Tafiyar ta ke da wuya mutanen da ke zaune gurin kowa da irin abunda yake cewa akan ziyarar bazata da ta kawo da irin yadda take da sakin fuska da fara’a ga kowa,
Muhammad Sani Ultimate ya bayyanwa Wakilinmu cewa lallai yaji dadin yadda wannan baiwar Allah ta nuna kauna da kulawa ga wannan masoyin nata, inda har ya yi kira ga Jarumar Finafinan Hausa akan su dunga kokarin nuna kulawa ga Mutanen da ke nuna masu kauna da soyayya.
A nashin bangaren Buhari Bross yace ba zai taba mantawa da wannan Ranar ba a tarihin rayuwarsa ace kamar shi, yadda yake san Bilkisu Shema ace sakwanshi ya kai mata a kunnuwanta, cikin ikon Allah taji har tazo yace bukatar ta biya.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button