Labarai

Shin Me ya Hada Musa kamarawa Aminin Bello Turji da Gwamnatin zamfara da Sokoto?

Shahararren marubucin nan Datti Assalafy yayi rubutu akan gwamnan jahohin sokoto da zamfara.

CIN AMANAR TSARO YA MUNANA A SOKOTO DA ZAMFARA

Kama abokin Bello Turji wato Musa Kamarawa da ‘yan sandan STS sukayi ba karamar nasara bace babba, abubuwa suna ta fitowa fili, duk wanda bai saurari jawabin Musa Kamarawa ba don Allah aje a saurara da kyau, na saka bidiyon a nan.

http://hausaloaded.com/2022/01/bidiyo-alhamdulillahi-an-kama-amini-abokin-bello-turji.html

Wannan da kuke gani a hoto tare da Maigirma Gwamnan Sokoto shine Musa Kamarawa abokin Bello Turji, kunji dai duk bayanan da Musa yayi a lokacin da ‘yan sanda suke tuhumarsa, ya tabbatar wa duniya cewa shi babban maciyin amanar tsaro ne, ya hada kai da Bello Turji yaci amanar al’umma kuma yaci amanar kansaShin Me ya Hada Musa kamarawa Aminin Bello Turji da Gwamnatin zamfara da Sokoto?

To amma wanene Musa Kamarawa da kuma tasirinsa?

Musa Kamarawa mutumin Sokoto ne, yana da alaka na jini da tsohon Gwamnan jihar Sokoto Bafarawa kamar yadda ya furta da bakinsa, Musa Kamarawa yaron Gwamnan Sokoto ne a yanzu, sannan kuma yana da alaka da Gwamnan Zamfara na yanzu, duka Gwamnonin sun bashi mukamin SA akan sha’anin tsaro

Gwamnan Sokoto ya bashi mukamin SA hakanan Gwamnan Zamfara, sunyi amfani dashi sosai akan matsalar tsaron jihohin nan guda biyu alhali yana matsayin babba aminin shugaban ‘yan ta’adda na yankunan, watakila ba da sanin Gwamnonin ba, watakila kuma da saninsu, wannan ba wanda ya sani sai Allah

Amma abinda ke akwai shine, a tambayoyin da ‘yan sanda suka yiwa Musa Kamarawa yayi bayanin cewa akwai wani abokinsa mai suna Daniel shi yake sayarwa su Bello Turji miyagun makamai, to zancen da nake muku yanzu haka har an bada belin Daniel, shima Musa Kamarawa ana hasashen manyan ‘yan siyasa na Sokoto zasu sa a bada belinsa

Kuma a cikin bidiyon da ‘yan sanda sukayi hira da Musa Kamarawa ya ambaci wani abokinsa Hashimu Kamarawa yana aikin sayarwa su Bello Turji kakin sojoji da na ‘yan sanda da takalma, Musa yace lokacin da ‘yan sanda suka sa ya kira Hashimu, a lokacin Hashimu yana cikin barikin sojoji na jihar Sokoto, har ma wani babban soja ya karbi wayan yake tambayar Musa Kamarawa a ina yake, abin tambaya me ya kai ‘dan ta’adda barikin sojoji?

Shin manyan barayi irin wadannan da sukaci amanar kasa sukaci amanar al’umma su wa ke sawa a bada belinsu imba ‘yan siyasa da wasu manyan jami’an tsaro da manyan Sarakuna ba?, idan hakane ashe duk ta’addancin da ake a Zamfara da Sokoto ajandace, watakila shiyasa Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zuba musu ido

Akwai wani kwamitin tsaro da aka kafa a Zamfara karkashin jagorancin tsohon shugaban rundinar ‘yan sandan Nigeria IGP MD Abubakar (mai ritaya) domin ya hada rahoto akan ta’addancin dake faruwa a Zamfara, kwamitin ya gama aikinsa, an samu manyan sarakuna da ‘yan siyasa da hannu dumu-dumu a ta’addancin, amma an hana a saki sakamakon bincike na Kwamitin, abinda ya faru kenan a Sokoto, akwai wani babban Basarake a Sokoto ya hana a fitar da sakamakon binciken ta’addancin dake faruwa

Kuma duk wannan abinda yake faruwa ba akan komai bane sai kudi, ‘yan siyasa sunci amanar al’umma, Sarakuna da suke wakiltar Musulunci sunci amanar Musulunci, sunci amanar Musulmai duk akan abin duniya mai karewa, da alama addu’ah da AlQunuti sun fara tasiri, asirin azzalumai maciya amana zai cigaba da tonuwa har a wayi gari sun rasa mafaka da ikon Allah

Muna rokon Allah Ya warware rawanin duk wani Sarki maciyin amana
Muna rokon Allah Ya kwace mulki daga hannun duk wani shugaban Gwamnati ko wakilin Gwamnati maciyin amana

Yaa Allah Ka amintar da bayinKa daga dukkan sharri da makircin makirai”

“BA WANDA YA SAN GASKIYA SAI ALLAH

Wannan itace takardan shaidar bawa abokin Turji Musa Kamarawa mukamin SA a Gwamnatin Zamfara

Kamar yadda zaku gani, a kwanan wata, an bashi mukamin SA tun a ranar 26-9-2019

Watakila Gwamman Zamfara bai sani ba ya bawa maciyin amana abokin ‘dan ta’adda mukamin SA, ba wanda ya san gaskiya sai AllahShin Me ya Hada Musa kamarawa Aminin Bello Turji da Gwamnatin zamfara da Sokoto?

Lokacin da ‘yan sandan STS suka saki bidiyon Musa Kamarawa bayan sun kamashi, akwai wadanda suke ganin rashin dacewar a saki faifan bidiyon saboda sun jahilci aikin Intelligence

Amma na tabbata zuwa yanzu an fahimci hikima da dalilin da yasa ‘yan sandan suka saki bidiyon

Muna rokon Allah Ya bamu mafita na alheri”

 

Shin Me ya Hada Musa kamarawa Aminin Bello Turji da Gwamnatin zamfara da Sokoto?

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button