Talakawa Sun Fi Shugabanni Rashin Imani A Najeriya – Sadiq Sani Sadiq
A wannan yanayi da ake ciki na dokar zaman gida da kuma azumi da al’ummar Musulmi ke dauke da shi a bakunansu, mutane da dama sun shiga cikin wani irin mummunan hali na kaka naka yi, sanadiyyar talauci da yunwa da mutane ke fama da ita.
Babban abin da ya kara haifar da wahala da ake fama da ita shi ne yadda kayan abinci da sauran kayan masarufi su kai tashin gauron zabi, ta yadda kusan komai an rubanya kudinsa a kasuwa.
To dama dai ko lokacin da babu wannan annobar, idan watan azumi ya kama sai kayan abinci sun kara kudi. Inda a zahirin gaskiya akwai rashin tausayi a cikin wannan abu da mutanen mu su ke yi.
Babban abin takaicin shi ne, ‘yan kasuwa da suke sayar da kayan, haka kawai suke kara kudaden, inda mafi akasari babu ruwan gwamnati a cikin wannan abu.
Wannan hali da ake ciki ne ya sa fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Sadiq Sani Sadiq, ya fito yayi magana, inda ya nuna rashin jin dadinsa akan lamarin.
“Abin nan yana damuna sosai, talakawan Najeriya bamu da imani, zaka ji mutane na cewa shugabannin Najeriya basu da kirki, shugabannin Najeriya mugaye ne, bayan mune matsalar Najeriya din.
“Kowa yana so ya samu hanyar da zai samu ya cuci dan uwansa, an kulle mutane a ko ina a Najeriya, amma komai yazo ya kara kudi, hatta ruwan ‘Pure Water’ ya kara kudi, shinkafa da ake nomawa a gida ita ma an kara mata kudi. Tumatir da ake sayarwa naira dari uku yanzu an mayar da shi dari shida.
“Ko kun gyara bamu damu ba, idan ma baku gyara ba bamu damu ba, addu’ar da muke shine Allah yasa mu samu rufin asirin da zamu iya ciyar da kanmu da iyalanmu koda kuwa kun kara kudin.
#labarai24