Labarai

Nace Nomiss Gee Wakilin Ibilis ne duk wanda bai dau mataki a kaina ba Allah ya tsinewa uban uwarsa – Aliyu Imam indabawa

Nace Nomiss Gee Wakilin Ibilis ne duk wanda bai dau mataki a kaina ba Allah ya tsinewa uban uwarsa - Aliyu Imam indabawaWani fitaccen mawaki a kafar sada zumunta ali imam indabawa yayi rubutu akan nomiss Gee Wanda mawaki ne na arewa hip hop kuma shine ke gabatarda shirin zafafafa goma a gidan talabijin na arewa24tv.
Wanda yayi rubutun ne a shekarar 2020 to shine kuma yanzu ya sake raddi Wanda alamu ya nuna cewa akwai wata a kasa.
Wannan shine asalin rubutun da yayi a shekarar 202.
“NOMIS GEE WAKILIN IBLIS A DORON KASA
A yanzu haka za’a iya cewa al’ummar Arewa ba ta da babban kalubale a gabanta ta fuskar tarbiyya da addini sama da wannan shaidanin yaro da a ke kira Nomis Gee.
Da ace mutanenmu na Arewa sun san yadda wannan yaro yake illata rayuwar yaransu ta hanyar lalata musu tunani ya hana su karatu da abin da zai amfani rayuwarsu ya shigar dasu mummunar harkar nan mara amfani ta wake-wake irin na gayun kasashen turawan yamma wacce ke haddasawa matasa shaye-shaye da zinace-zinace da kazamar harkar nan ta neman maza wa’iyazubillah.
Da mutanen Arewa sun san barnar da wannan shaidanin yaro yake wa yaransu da tuni sun shiga sun fita sun dauki mataki a kansa, muna da masaniyya yadda wannan yaro yake illata mana al’umma ta hanyar bin matasa har da ‘kananan yara yana kwadaita musu wannan mummunar harka yana shigo da su ta hanyar haska su a shirin da yake yi gidan Tvn Arewa24, shirin da babu abinda ake nunawa sai badala da alfasha, ta yadda ake nuna mace musulma bahaushiya tayi mummunar shiga kanta babu dankwali ana ganin saman nonuwanta ga cikinta da cinyoyinta a bude, tana rawar banza ta Allah wadai, ka ga Namiji yayi tatoo yayi ass down shiga ta mashaya masu neman maza.
Tuni mun jima da gane gidan Tvn Arewa24 kwangilar yahudawa ce domin raba al’ummar arewa da addininsu, wallahi hatta wani ma’aikacin gidan ya tabbatar min da haka.
Muna ba wa iyaye shawara da su kula da tarbiyyar yaransu, su kuma daina kunna musu munanan shirye-shiryen wannan tasha, kuma su yi amfani da wannan dama ta wannan wata mai albarka su kai karar wannan mutumi me suna Nomis Gee wajen Allah, har ma gidan arewa24 kamar yadda muke amfani da wannan dama mu yi addu’a a kan bala’in Coronavirus.
Muna kira ga gwamnatin Kano da ta baiwa Hukumar tace fina-finai cikakken goyon baya domin daukan mataki a kan wannan shaidanin yaro da shirin da yake yi dama tashar baki daya.
Allah ka ci gaba da tonawa Arewa24 asiri tare da sauran makiya addinin musulunci.
Indabawa Aliyu Imam”
wanda a yanzu ya sake yin magana mai zafin gaske akan adinda ya rubuta
“An fada din Nomiis Gee wakilin Iblis a doron kasa, wanda ya fasa daukan mataki a kaina Allah ya tsine wa Uban uwarsa. Ba wanda ya fi ni zafin kai da taurin kai, rigima ma da kudi nake siyanta. Allah ya tsine wa wanda ya fasa don ubansa”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

  1. Gaskiya ka fada Dan uwa dan walahi ban taba shaawar wannan kalon Shirin ba domin tunda aka fara na fahinci Anya wannan kuwa ba wane Abu sukeso su aka a cikin al,umma ba to kukan kuciya jawabine ga Yan arewa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button