Babu namijin da ya taba zuwa min da maganar aure – inji Jaruma
Wata matashiyar jarumar fim ta bayyana cewa babu wani namiji da ya taɓa tunkararta da maganar aure, kuma dama tana ganin cewa har yanzu bata kai munzalin da zata yi aure ba.
Jarumar tana Sakandire ta fara harkar fim
Sharon Ifedi jarumar fim ce dai ta kudancin Najeriya wacce ta fara taka leda a harkar wasan kwaikwayo tun a lokacin da take a sakandire. Sai dai tana ganin kamar har yanzu shekarun ta basu kai ba na wanda za’a ce tayi aure.
A wata tattaunawa da majiyar mu ta samu, jarumar tace a can baya tayi ƙudurin ta karanci ɓangaren aikin likitanci ne kafin daga bisani kuma ta tsinci kanta a harkar fina-finai.
Da aka tambaye ta ko an taɓa yi mata tayin aure ba ta amsa ba a waɗannan shekarun nata? Jarumar ta bayyana cewa bata taɓa ba, sabili da a cewar ta babu wani wanda ya taɓa tunkararta da maganar cewa yana son ya aure ta. Shafin Labarunhausa na ruwaito
Tafi maida hankali kan harkokin fim
Jarumar ta ƙara da cewar dangane da kuma irin namijin da take so, wannan idan lokacin da take ganin ta isa aure yayi zata duba ta gani, tunda a yanzu dai bata san komai ba dangane ga maza.
Ta kuma ƙara da cewar yanzu tafi maida hankali kan sana’ar ta ta fim. Bata alaƙa ko soyayya da kowa. Duk da dai ta tabbatar da cewa akwai mazaje da dama da suke son ta.
Da aka tambayi jarumar kan ko wane irin ƙalubale ne take fuskanta a harkokin ta na wasan kwaikwayo a matsayin ta na jaruma mai ƙaranci shekaru. Jarumar ta bayyana cewa abinda ke takura mata shine, yanayin yadda take baro ‘yan uwanta a gida tun da sassafe ta tafi wajen ɗaukar fim, ba zata dawo ba a wasu lokutan ma sai dare.
Sai dai tace babban ƙalubalen da a yanzu take fuskanta sune sauran matakan da bata taɓa fitowa ba a cikin finafinan da take yi. Tace a matsayin jaruma yana dakyau ace mutum ya iya fitowa a matakai da dama.
Wani ya taɓa rungume ta a tsakiyar jama’a
Ta bayyana cewa wani abu kuma da yakan ɓata mata rai shine yadda wasu daga cikin masoyanta ke yi mata a yayin da suka ganta. Tace akwai lokacin da wani daga cikin masoyanta ya taɓa zuwa ya rungume ta a wajen wani taro da har sai da mutane suka janye shi daga jikin ta.
Daga ƙarshe ta bawa jarumai mata masu tasowa shawara kan su riƙa ƙoƙarin baiwa kansu atisayen fitowa a fim kafin ma suje gaban furodusa. Tace hakan zai taimaka musu sosai.