Labarai

Allah ya isa tsakanin mu da Buhari – Audu Bulama Bukarti

Allah ya isa tsakanin mu da Buhari – Audu Bulama BukartiBarista Audu Bulama Bukarti, mai bincike kan harkokin tsaro a cibiyar Tony Blair Institute da ke ƙasar Burtaniya ya bayyana cewa tsakanin al’ummar Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari sai dai Allah ya isa.
Audu Bulama Bukarti wanda gogaggyen lauya ne ɗan asalin jihar Yobe, ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a shafinsa na Facebook.
Haka kuma lauyan ya ce muddin al’ummar Arewacin Najeriya ba su farkar da Buhari daga baccin da ya ke yi ba to tabbas haka za a yi ta kashe su, shi kuma shugaba Buharin yana ta sharholiyarsa.
Wato idan dai ƴan Arewa ba za su tashi su farkar da Buhari ba, to haka za ayi ta kashe mu, shi kuma yana sharholiyarsa. Rai da mutunci da dukiyar musulmi da ƴar Musulmi da ɗan Musulmi sun zama ba a bakin komai ba. Yanzu da a ƙarƙashin shugabanci ɗan Kudu ake mana haka, haka zamu yi? Me ye amfanin na kan da ya ƙi tsare ranka ma da mutuncinka da dukiyarka? A jahiliyar da ma ba a yi irin wannan rashin Imanin ba. Shi kuma yana can sai yawon banza da wofi, wanda bai amfane mu da komai ba. Allah Ya Isa” In ji Barista Audu Bulama Bukarti
Haka kuma lauyan ya bayyana cewa daga can birnin Landan su na can su na shirye-shiryen matakin da za su ɗauka akan yadda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi wasarere da rayukan al’umma musaman yankin Arewacin Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari da Barista Audu Bulama Bukarti a shekarun baya

Ga masu tambayar cewa me za su iya yi, wa zai iya fitowa zanga-zanga ko zaman dirshan? Wa zai iya shirya al-kunutu gobe Jumu’ah? Kowa ya shirya abinda zai iya a inda yake. Mu ma nan muna tattaunawa akan abinda zamu shirya
“#BuhariAllahYaIsanmu

BuhariAllahYaIsanmu

BuhariAllahYaIsanmu”.

Tuni dai ƴan Najeriya su ka fara bayyana suƙewa game da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ƙazanta a arewacin ƙasar nan yayin da ake zaman makokin wasu ƴan cirani fiye da 40 da ƴan bindiga su ƙone su ƙurmus a ƙauyen Gidan Bawa da ke Sokoto.
Babu shakka girman matsalar tsaro na ci gaba da ƙonawa jama’a gyaɗa a tafin hannu, kuma hakan ya sa fushin jama’ar yankin arewacin ƙasar ya fara bayyana ƙarara.

Yanzu haka dai hankulan mafi yawan mutanen arewacin Najeriya a tashe yake, da alamu kuma an kai su bango, dangane da yadda matsalar ta tsaro ke matukar ci masu tuwo a ƙwarya.
Ya kara ka cewa Barista Audu Bulama Bukarti
Wato Buhari da ‘yan kanzaginsa ba za su gane kuskurensu ba sai mulki ya ku6uce. Yanzu da wanne ido zamu kalli wani shugaba daga Kudu mu nemi ya gyara mana matsalar da namu ya kyale tsawon shekara takwas? Idan Buhari ya sauka bai gyara yanayin tsaro a Zamfara da Kaduna da Sokoto da Neja da jaharsa Katsina ba, Bayerabe ne ko Inyamuri zai zo ya gyara mana? Idan Buhari bai damu da ranmu ba, wani ne zai zo ya damu da mu? Wallahi, sai mulki ya ku6uce zamu gane kurenmu. ‘Yan kujeru da ‘yan kudaden da ku ko iyayen gidanku ke samu yanzu duk za su kare nan da ‘yan shekaru.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button