Kannywood

Aminu saira ya fara shan suka game da fim ɗin Labarina

Aminu Saira Ya Fara Shan Suka Game Da Fim Ɗin Labarina
Aminu Saira

Ma’abota kallon shirin nan mai dogon nan, wato Labarina, sun fara sukar Daraktan Shirin, Aminu Saira, game da yadda shirin yake tafiya a halin yanzu.
An fara nuna shirin Labarina ne ranar 6 ga Yuli, 2020, kuma kawo yanzu ana zango na huɗu ne a shirin.

Shiri ne da a farko ya ja hankalin mutane sosai tare da shan yabo daga mutane da dama.
Sai dai a cikin zango na huɗu na shirin ne aka nuna Nuhu Abdullahi (Mahmud a cikin shirin) ya rasu, kuma aka nuna an yi garkuwa da Nafisa Abdullahi, (Sumayya a cikin shirin).
Za a iya cewa waɗannan jarumai biyu su ne manyan taurari a farkon shirin.
An shafe kusan makonni biyar ba a nuna an ceto Sumayya daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da ita ba.

Aminu Saira Ya Fara Shan Suka Game Da Fim Ɗin Labarina
Aminu saira Daraktan Shirin Labarina

Abubuwan da za a iya cewa sun ɓata wa masu kallon shirin rai su ne: mutuwar Mahmud, yin garkuwa da Sumayya da kuma kasa ceto ta.
Labarai24 ta ci karo da wasu wallafe-wallafe da ma’abota kallon shirin suka yi a shafukan sada zumunta- wallafe-wallafen da suke nuna suka da kuma ƙosawa da kallon shirin.
Ga kaɗan daga ire-iren ra’ayoyin jama’a game da shirin.

Arewa Queen ta ce: “Labarina writers are out of ideas. I think that guy fathered every young chap in the series except Presido.
“Dabara ta ƙarewa marubuta shirin Labarina. Ina jin wannan mutumin shi ne ya haifi duk wani matashi a shirin banda Presido”.
Safiyanu Z Yusuf Danman cewa ya yi:
“Malam Aminu saira is gonna destroy his VALUE
“He has been one of the most talented, right thinking director. But With the way he’s playing with our sense in LABARINA, I started losing confidence in him. Those who are close to him should call him to order before he gets lost”.

Aminu Saira Ya Fara Shan Suka Game Da Fim Ɗin Labarina
Nuhu Abdullahi Jarumin Labarina

“Malam Aminu Saira yana shirin zubar da kimarsa. A baya ya kasance ɗaya daga cikin daraktoci mafiya hikima da tunani. Amma bisa yadda yake wasa da hankalinmu, na fara dawowa daga rakiyarsa. Ya kamata waɗanda suke kusa da shi su jawo hankalinsa kafin ya ɓata”.
Comr Ibrahim Suleiman Ibrahim ya ce:
“That’s the problem with all these Hausa series. Too much prolongation of their series is what usually result to this.

“I could vividly remember in 2019 how I started following the kwana casa’in series, until they finished season 1 and 2, then they started messing with my intelligence, which made me stop watching it. Same applied to Labarina, I stopped watching the series 3 episodes after “Baba Dan Audu” was introduced.
“They keep making the mistake of prolonging series films without rich ideas on how to continue with the story they started”.
“Wannan shi ne matsalar waɗannan finafinan na Hausa masu dogon zango. Jan labari ba gaira ba dalili shi ne yake haifar da wannan. Zan iya tuna yadda na fara kallon Kwana Casa’in a 2019, lokacin da suka kammala zango na 1 da na 2, sai suka fara raina min hankali, abin da ya sa na daina kallon sa kenan. Irin abin da ya faru da Labarina kenan. Na daina kallon sa zango uku bayan an shigo da Baba Ɗan Audu.
“Sukan yi kuskuren jan fim ba tare da dabarun yadda za su ci gaba da labarin da suka fara bayarwa ba”.
Nura I. Sodangi ya ce:

“Wallahi sun yi muguwar kwafsawa. I was telling a friend lokacin da abubuwa suka ƙare ma Mahmud, lokacin da ya yi asarar Laila da ita Sumayya ɗin da kuma ganowar cewa shi shege ne, to a kulle labarinsa da na su laila ɗin. Sai a ɗauko wani sabon labarin cakwakiya da ita Sumayya za ta faɗa. Ba laifi a ci gaba da tafiya da ‘yan kaɗan kamar su Presido da Lukman jifa-jifa.
“Amma sam sai na ga wai sun zarce da su Mahmud ɗin. Sai na ce wallahi za su carke”.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

3 Comments

  1. I can’t continue watching long film without educative ideas. I have since stoped watching Labarina and may soon discontinue with Izzar So and probably Kwana Chasa’in

  2. Ni a gani na salon yadda Aminu Saira ya ke nunawa a cikin shirin labarina ya dace domin ita Sumayya ita ce ta ke rike da jigon labarin duk wanda ya fito a shirin me raka ta ne ta kai sakon labarin inda ake so ta kai shi saboda haka warwarar jigon zai dinga tafiya ne kadan-kadan saboda haka dole za’a ga abin ya na tafiya a hankali a haka ne mashiryin shirin zai kai mai kallo inda ya ke so ya kai shi kamar mutuwar Mahmud shi labarin sa ya kare akan ita Sumayya saboda ita ce jigon kasancewar ta a hannun ma su garkuwa da mutane ba shi ne kadai abinda ya rage ba Mahmud ya taka irin rawar sa ta soyayya har ya tserar da ita daga hannun wanda ya nemi ya fada rayuwar ta a sanadin rashin lafiyar mahaifiyarta shi kuma Lukman ya taka irin ta sa rawar shi kuma presdor sai a saurari irin yadda zai taka ta sa rawar me yiwuwa a wannan gabar zai ta ka ta sa rawar da kuma wasu ragowar kananan jigogin labarin saboda haka dole abin ya dau lokaci wallahu aalam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button