Kare mutuncin Rarara Yafi min Neman takarata – Alan waka
Shahararren mawakin nan Aminu Abubakar Ladan wanda anka fi sani da alan waka ya fito ya bayyanawa duniya cewa kare mutuncin Dauda Kahutu Rarara yafi masa fiye da takarar dan majalisar tarayya da yake kamar yadda ya wallafa a shsfinsa na sada zumunta.
“Yaƙin kare mutuncin Dauda ya fi yaƙin neman zaɓen ɗan takarar ɗan Majalisar tarayya agareni.
Mu yi mutunci da mutuncinka, ka yi mutunci da mutuncinmu shi ne babban arziƙi na zaman tare.
Takarata fansa ce a wajen kare mutunci da Hakkin DAUDA.”
Wanda kafin ya wallafa wannan rubutu mawakin yayi rubutu masu hikima da azance wanda yake daurewa mutane kai sosai wanda abun ya baiwa mutane mamaki sosai kamar inda ya sanya wannan rubutun a jikin hoton dauda kahutu Rarara.
“Kallo ya koma sama fa dukkan alamu
Mugun madambaci shagon Guramaɗa.
Da yawa daga masu faɗa da kai ba su san abokin faɗan su ba. Haƙika da sun sani da basu yarda sun gwadawa kuciyya baka ba.”