Zuwa Zancen kafin Aure – Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Zance da ake yi tsakanin masu neman aure domin su ga juna su tattauna, su gabatarwa da juna buƙatar aure da kuma neman amincewa da soyayya, da fahimtar juna,
Amma a kula yadda ake zance yanzu akwai fitsara sosai yadda ake rungume juna da taɓa jiki, da yin abubuwa masu muni wani lakacin har da saduwa kafin aure,
Duk wanda ta yarda wani ya taɓa mata jiki to ya gama ita domin ba za ta ƙara mutunci a wajan sa ba.
Malamai sunyi saɓani akan iya gurin da ya kamata mai neman aure ya gani a jikin matar da zai aura
Iya faɗin fuska da tafin hannu.
Iya shiga ta al’ada da zaman gida
Duk inda zai ja hankalin sa zuwa ga auran ta
Amfanin zuwa zance ko ganin mace domin gabatar mata da kai, a matsayin mai neman aure, shi ne abin da malamai suke kira neman aure ko kuma kiɗbah, asali ana neman auran mace a wajan waliyinta a mataki na farko domin samun iznin ganin ta da tattaunawa da ita, don samun fahimta, kamar yadda Manzon Allah saw ya nemi auran Aisha a wajan mahaifinta Abubakar. Bukhari 5081.
Mataki na biyu, ana iya neman auranmace kai tsaye a wajan ta idan mai hankali ce, kamar yadda Annabi saw ya nemi auran Ummu Salamata a wajan ta, har ta bayar da uzrin yawan ƴaƴa da shekaru da tsananin kishi, ya bata amsa da zai riƙe mata ƴaƴan, shekaru kuma shima yana da su, kishin kuma zai roƙi Allah ya rage mata shi, Muslim Annasa’iy.
Mataki na uku Mahaifin mace ko waliyinta zai iya gabatar da ita ga mutanan kirki, domin sama mata miji, kamar yadda S. Umar ya gabatar da Ƴarsa Hafsah ga S. Abubukar, sannan Usman daga baya Manzon Allah saw ya aure ta. Bukhari 5122. Da hadisin Umma Habibah da ta nemi Manzon Allah saw ya auri ƴar’uwarta, ya nuna mata baya hallata a musulunci haɗa ƴan’uwa a igiyar aure ɗaya a lokaci ɗaya. Bukhari 5107.
Mataki na hudu ya halatta mace mai hankali ta gabatar da kanta da wani mutum nagari ko zai amince ya aure ta, kamar yadda wata mata ta gabatar da kanta ga Manzon Allah saw, ko zai amince ya aure ta, Bukhari 5120.
Mataki na hudu wani ya na iya zama sila ko dalili wajan shige wa gaba wajan kulla alaƙar aure tsakanin masu neman aure kamar yadda kaulatu Bnt Hakeem ta gabatarwa da Manzon Allah saw auran Nana Saudah bayan wafatin mijinta.
Mataki na biyar za a iya kafa wata ƙungiya mai ɗauke da amintattun mutane masu ilimi da sanin haliyyar jama’a, su ɗinka zama masu dalilin aure, duk mai neman aure mace ko namiji sai ya je gurinsu, domin tantancewa da shigewa gaba wajan haɗa aure.
Mataki na shida za a iya buɗe wata kafa a Internet a buɗe Web site, domin wannan aiki amma yana buƙatar aiki da saka ƙaidoji domin ka da a canga munufar buɗewar zuwa wani abu daban.