Addini
Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bada Tallafin Naira Milyan 25 Ga Gidauniyar Sheikh Sharif Saleh Maiduguri (Cikin Hotunan)
Daga Rayyahi Sani Khalifa
A yau 29 ga watan Satumba aka bude taron gidauniyar Maulana Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Maiduguri mai taken SHEIKH SHARIF SALEH ISLAMICCENTRE (SHISIC), a dakin taro na National Conference Centre dake Abuja.
Taron ya kunshi manyan jami’an gwamnati da masu hannu da shuni, inda manyan baki suka yi ta bada gudunmawa.
A nasa gudununmawan Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi a madadin shi kansa da iyalansa ya bada gudunmawan kudi naira milyan ashirin da biyar (25,000,000)
Allah ya sa albarka a wannan aikin alkairi, amin.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com









![[Tafsirin Surah Âl-`Imrân:] - Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2022/04/FB_IMG_1649081565215.jpg?resize=390%2C220&ssl=1)