Kannywood

Hadiza Gabon Ta Soki su Ali Nuhu kan shishigin da sukayiwa Jaruman Big Brother

Advertisment

Hadiza Gabon Ta Soki su Ali Nuhu kan shishigin da sukayiwa Jaruman Big Brother A ranar lahadin da ta gabata aka kamala shirin big brother naija kashi na shida wanda aka shafe sama da watanni ukku ana yin shirin da ake haskawa a gidan talabijin na startime,inda wani inyamuri mai suna whitemoney ya samu nasarar lashe gasar da akayi ya samu zunzurutun kudi naira miliyan 90.
Wannan shiri ya samu kalubale daga malaman addini da masu fadakarwa na musulunci da na kiristoci duba da yadda ake gudunar da al’amura da suka ci karo da koyarwa adinan biyu sai dai fa matasa da har ma da wasu masu shekaru sun raja’a kallon shirin da kuma bibiyar sa duk da tabatsalliyar da ake ciki.
Jim kadan bayan kammala wannan shiri zakaran da ya lashe gasar da me bi masa da wassu daga wayanda suka kasance cikin shirin sun yiwa kano tsinke domin wani shagalin taya murna da kamfanin multichoice masu Dstv da go tv suka shirya musu inda aka gabatar da taron shagalin a dakin taro na tahir Guest palace da ke kano.
Jaruman kannywood sun samu hallatar wannan taro sunyi hotuna da bidiyo taya whitemoney murna cikin wayanda suka samu hallatar sun hada da ali nuhu, adam a zango , Abubakar mai shadda hazir dan hajiya, Almustpha, baba karami, Ibrahim mindawari da dai sauransu.
Ga cikakken bayyani nan a cikin faifan bidiyo

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button