Uncategorized
Kotu Ta Yankewa Dan Shah Rukh Khan Hukuncin Kwana 14 A Gidan Yari
WASHINGTON D.C. — Wata kotun Mumbai a India ta yankewa Aryan Khan, da ga jarumin Bollywood Shah Rukh Khan, hukuncin zaman gidan yari na tsawon kwana 14.
An yake masa hukuncin ne bayan da aka same shi da laifin mallakar miyagun kwayoyin tare da wasu mutan bakwai a wajen wani shagali da suka shirya a irin jirgin ruwan nan na alfarma.
A ranar Asabar aka kama Khan da mutanen bayan da aka kai samame cikin jirgin ruwan na alfarma a can gefen gabar tekun birnin Mumbai a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.
Shekarun Aryan Khan 23, shi ne kuma babban dan tauraron na Bollywood.

An tsare shi ne bisa tsarin shari’a da zai kasance karkashin kulawar kotu maimakon hukumar da ke kula da ayyukan gyara hali.
Dan shekara 55, Shah Rukh Khan na daya daga cikin fitattun jarumai a duniya, wanda ake wa lakabi da “King of Bollywood,” wato “Sarkin Bollywood.”
Ya kwashe kusan shekara 30 yana wasan kwaikwayo a dandalin shirya fim na Bollywood inda ya fito a fina-finai sama da 105.
Shah Rukh na da mabiya sama da miliyan 42 a shafin Twitter, shi ne kuma mamallakin kungiyar wasan kulki ta cricket da ake kira “Knight Riders” da ke buga wasa a gasar Indian Premier League – gasar wasan cricket da ta fi armashi a duniya.