Yanzu yanzu: Dan Sarauniya ya nemi afuwar Sheikh Kabiru Gombe
Daga karshe dai muazu magaji win win ya bada hakuri ga shehin malami sheikh kabiru gombe akan magana da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta wanda kuma sheikh kabiru gombe ya nuna cewa ya janye kalamansa cikin awani 12 ko su gurfana a gaban kotu.
Inda wani shafin kano sunka wallafa bada hakurin wanda shi muazu magaji yayi sharing a shafinsa ga abinda sunka wallafa.
“Biyo bayan wa’adin awanni 12 da babban malamin addinin musulunci kuma sakataren kungiyar IZALA na kasa Sheik Kabiru Gombe ya bayar, na cewa tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Muaz Magaji Dan Sarauniya, ya janye kalamansa na cewa Malamin yace zasu fice daga jam’iyyar APC mai mulki, matukar dai aka janyo tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso cikin jam’iyyar, wanda yace ba Gaskiya bane, domin shi ba dan siyasar jam’iyya bane, saboda haka zai tafi kotu neman hakki.
Jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, tuni Dan Sarauniya ya nemi afuwar malamin, da kuma bashi hakuri akan abinda ya faru, domin shima a wata jaridar yanar gizo mai suna Punch Hausa yaga an buga labarin, shi yasa ya kwafo ya wallafa domin nusar da kuskuren abin, saboda bai dace malamai da sarakuna su dinga daukar bangarenci na ra’ayin siyasa ba, haka zalika yace ya dauki darasi na rashin makala inda ya samo rubutun, a saboda haka itama jaridar Punch Hausa yana neman afuwarta.


“Mallam Kabiru Gombe, sakon Allah wadai da kai kan labarin da na gabatar, ina mai baka hakuri da neman afuwa, kuma ina sanar dakai cewa ba nine na kirkiri labarin ba, Jaridar Punch Hausa ne suka buga shi, ina ganin yanzu ka fahimci hakan don naga anja hankalinka ga hakan, wallahi sam bana son Malami ko Sarki na fitar da ra’ayi kururu a siyasa irin tamu ta Nigeria don nasan illar da za ta iyayi mana a addinance da Al’adance, don haka nai sharing labarin don Jan hankali. Amma in ba kai kayi wannan maganar ba to don Allah kayi hakuri, in kuma ajizan ci yasa kayi to a guji gaba don amana tayi karanci a siyasa.” ~ Muaz Magaji
Mutane da dama sun bayyana ra’ayinsu tun farkon faruwar lamarin har yanzu da a iya cewa yazo karshe, kuma Muaz Magaji ya samu yabo daga mutane da dama, bisa ga yadda ya nuna dattako ya nemi afuwa akan abinda ya samo daga wani waje daban, wanda ba’a cika samun mutane masu saukin kai wajen karbar gyara ko korafi akan wani abu ba, amma shi cikin sauki ya tabbatar da cewa ba aikinsa bane taba malamai ko sarakuna, sai dai idan harkar siyasarsu suka shigo.
Daga: Kano Online News
10/9/2021.”
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)



