Labarai

Cin Fuskar Musulunci : Tsinanniyar Da Ta Kalubalanci Hukuncin Kisa Ga Wanda Ya zagi Annabi , Kungiyar Lauyoyin Nigeria NBA Sun Gayaceta Matsiyin “Speaker” A wajen Taron Kasa

Advertisment

Kungiyar lauyoyin Nigeria, Nigeria Bar Association (NBA) bisa jagorancin Mr Paul Osoro (SAN) ba shakka ta nuna wa Musulunci da Musulmi wariya da kuma kiyayya, dalilin fadin haka shine:

Kungiyar lauyoyin, a shirin da take na gabatar da babban taro da ta saba gabatarwa duk shekara, to a wannan shekaran ma zatayi taron, kuma cikin wadanda aka gayyata zasu gabatar da jawabi akwai gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai

To sai aka samu wasu Lauyoyi makiya Musulunci wadanda ba musulmai ba suka mika sakon koke zuwa ga jagorancin kungiyar ta Lauyoyi cewa ba su yarda Malam Nasir El-Rufai ya halarci taron ba, saboda wai ya sa ido ana kashe wasu mabiya addinin da ba na Musulmai ba a kudancin Kaduna

Wanda a zahiri babu mutanen da akafi kashewa a kudancin Kaduna kamar Hausa/Fulani/Musulmai, to amma saboda kin Musulunci sai aka cire sunan Malam Nasir El-Rufai din, wato aka nuna mana tsantsan wariya da banbancin addini

Advertisment

Ba mu huce da wannan cin fuska da NBA ta mana ba a matsayin mu na Musulmai, abin takaici kwatsam yau sai naci karo da wannan takarda wai NBA ne ta turawa yarinyar nan mulhida Fakhariyya  Hashim sakon gayyata, tana cikin wadanda aka gayyata a babban taron na NBA

Idan baku manta ba jama’ar  Musulmi, Fakhariyya Hashim itace wacce kwanaki ta goyi bayan cin zarafin Manzon Allah (SAW) bayan da kotu ta zartar da hukuncin kisa ga wanda ya zagi Manzon Allah, sai Fakhariyya ta fito ta kalubalanci hukuncin, tace wai bai kamata a kashe wanda ya zagi Annabi Muhammad (SAW) ba, wai take hakkin bil’adama me

Datti assalafy ya cigaba da cewa Kowa ya san da abinda Fakhariyya ta mana wanda ya taba zuciyar duk wani Musulmi, abune da ya yadu sosai, wato domin jagoranci NBA ta kara bakanta ran Musulmai; sun cire sunan ‘dan uwan mu Musulmi daga taronsu, sai gashi sun gayyato wanda ta kaskantar da darajar Annabin mu

Muna kira ga ‘yan uwa Musulmai lauyoyin Nigeria, yadda lauyoyin da ba Musulmai ba suka soki gayyatar da aka yiwa ‘dan uwanmu Musulmi Malam Nasir El-Rufai har aka cire sunansa, to muna rokon ku Lauyoyi Musulmai don girman Allah ku fito ku soki gayyatar da aka yiwa la’ananniya Fakhariyya Hashim

Kuma ya zama wajibi dole, tilas ga duk wani Lauya Musulmi ya gujewa halartan taron NBA na kasa da za’a gabatar muddin ba’a cire sunan tsinanniya Fakhariyya ba, kowa ya fahimci cewa yakar Musulunci ake yi ta ko’ina, ya zama wajibi mu hada kai mu kwaci ‘yan cin mu a gurin makiya

Yaa Allah Ka saka mana bisa wannan cin fuska da aka mana

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button