Allahu Akbar : Senator Ahmad Babba kaitabya bada Umurnin a amshi CV din kawu malami raduate din Agricultural Engineering da ke sana’ar tura ruwa
Alhamdulillahi jiya idan baku manta ba munkawo muku labari mai ban Tausayi na wani bawan Allah wanda yayi karatu amma bai samu aiki ba da yake babu mutuwar zuciya sai gashi babban mutumin shugaba wanda ake bukata a wannan zamani senator Ahmad Babba kaita ya aikata alkhairinsa kamar yadda Malam Ibrahim Bature ya wallafa a shsfinsa na sada zumunta yana mai cewa :
Senator Ahmad Babba Kaita ya bada Umarnin a amshi CV din Kawu Malami, Graduate din Agricultural Engineering din nan wanda rashin aiki yasa ya fara tura kurar Yana sayar da Ruwa.
Kawu dai tun 2014 ya kammala karatun sa a UNIMAID, Bai samu aiki ba. Dukda kasancewa shi Dan Bauchi ne, Amman Sanatan Sanatochi, Borderless Senator ABK, yasha alwashin, idan dama ta samu zai bashi aikin yi.
Allah ya saka wa Distinguished Senator Ahmad Babba Kaita da alkhairi. Allah ya Kara wadata mana su cikin al-ammah, Amin.


Shiga wannan link domin Karanta hira da rayuwar wannan bawan Allah da takardar dunsa.