Kannywood

Mun Haramta haska fim da aka nuna yadda ake garkuwa da mutane – Afakallah

Mun Haramta haska fim da aka nuna yadda ake garkuwa da mutane – Afakallah
Ismail Na Abba Afakallah

Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano ta haramta haska duk wasu fina-finai da aka nuna yin garkuwa da mutane.
Hukumar ta ce, ta haramta nuna fim da haska yadda ake sayar da ƙwayoyi ko kuma shan kwayoyin maye.
Shugaban hukumar Alhaji Isma’ila Na’abba Afakalla ne ya bayyana haka, zantawar sa da Freedom Rediyo.
Duk Film ɗin da aka nuna yadda ake kwacen waya a hannun mace, ko namiji ko wata mummunar ɗabi’a, shi ma ba za mu amince a haska shi ba”.
Afakallah ya kuma bukaci ƴan jarida da su taimakawa hukumar wajan wayar da kan al’umma domin dakile irin waɗannan matsaloli da aka iya gurɓata tarbiyyar matasa da ci gaban Rayuwar su.
Ismail afakallah yayi wannan ne domin ganin cewa fina finai na masu garkuwa da mutane yana taimawa wajen kara yaduwar garkuwa da mutane wanda wannan abu ne marar kyau a cikin al’umma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button