Kannywood

Ta yi Watsi Da Harkan Film, Ta Burgeni Matuka ~ Datti Assalafy

Advertisment

Kamar yadda naga kamfanin jaridar Zinariya sun kawo labarin wannan matashiya Zahra Diamon da take harkan Hausa film tayi watsi da wasan kwaikwayo tayi aure ta kama hanyar tsira a duniya da kuma lahira
Ance Zahra ta fitar da wasika ga masoyanta kamar haka:
“Salam masoyana, producers ɗina, directors da abokan aikina, waɗanda na gama ayyukansu ina musu fatan alkairi, waɗanda kuma ban gama ba ina mai ba su haƙuri, saboda yanayin zaɓin da Allah ke yiwa dukkanin bayinsa, to yamin zaɓi mafi alkairi a gareni, saboda haka bani da baki ko ‘yancin ƙarasa muku ayyukanku. Fatan zaku fahimceni? Allah ya baku haƙuri ya kuma musanya muku da alkairi”.
Sannan ta ƙara da cewa, “Dan Allah masu fans Fage ɗina, kuyi haƙuri ku dubi girman Allah ku cire hotuna ɗina, da kuma bidiyo-bidiyo ɗina, kuma ku canza sunana, nagode”.
Tsakanina da Allah ni Datti Assalafiy naji dadin wannan labarin, kuma na tayata murna da farin ciki da tayi watsi da sana’ar film da kuruciyarta kafin bakaken kuraye su tarwatsa mata rayuwa
Wallahi ba karamin hatsari bane matashiya kamar wannan ta baro Kasarta Nijer ta shigo Nigeria ta tare a gurin ‘yan daudu da kawalai tana wai sana’a, gurin da babu iyayenta babu kowa nata
Kwanaki BBC Hausa sunyi hira da ita, anyi mata tambayoyi tana bada amsa, har aka tambayeta menene burinki a rayuwa? sai tace burinta shine ta shahara a harkan film domin ta samu kudin da zata rufawa kanta asiri
Kawai sai tausayinta ya kamani a lokacin, domin na san dai duk wanda ba Director bane yace zai rike film a matsayin sana’a don ya samu kudi kansa yake yaudara, ba’a kudi a shirin film sai dai ayi talla a kauce hanya a rungumi sana’ar banza ta bayan fage
Duk wanda ya karanta sakon Zahra zai fahimci ta auri mutumin kirki ne mai addini, shiyasa ta roki masoyanta su cire hotuna da bidiyo dinta domin ta kare mutuncin kanta da na iyalanta da zata haifa nan gaba, muna fatan wannan zai zama babban darasi ga su Rahama Sadau da sauran mata masu gigiwa
Muna fatan Allah Ya sanya albarka a cikin auren Zahra, Allah Ya basu zuriya mai albarka wanda duniya zatayi alfahari dasu Amin

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button