Dangin miji ne su ke kashe mana aure, – Inji Jaruma Ummi Gombe
Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood Hadiza Abubakar, wacce aka fi sani da sunan Ummi Gombe. Ta bayyana yadda dangin miji su ke raba su da mazajen da suka aura a matsayin su na yan fim.
Ta kara da cewa,hakan ya na matukar kawo musu matsala a duk lokacin da suka yi aure, kamar yadda ita ma ya faru da ita.
Ummi Gombe ta bayyana hakan ne a hirarta wakilin jaridar Dimokuradiyya.
Kazalika ta ce, “Ka san mu yan fim, mu na da farin jini, kuma muna da bakin jini” inji ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: A Na Muna Zargin Yan Iska Muke – Jaruma Amal Umar
“Domin duk yar fim din da ta yi aure takan samun irin wannan matsalar, wani lokacin ba tsakanin ta da mijin ba ne, sai ka ga, kin yi aure mijin ki yana son ki, ke ma kina son sa, amma yan uwan sa, musamman mata, sai su dauki karan tsana su dora miki” a cewar Ummi.
Kazalika ta cigaba da cewa, “Don gaskiya yan fim suna fuskantar matsala a wajen dangin miji, sai ka ga ba wani abu ka yi musu ba, amma in dai ke yar fim ce, sai kawai su tsane ki”
“Da haka za su hura wuta har sai ya sake ki, kuna son juna, haka Zaki rabu, babu yadda za ku yi, dole ku rabu”
“Don haka mu yan fim idan muka yi aure sai ka ga an tsane mu, an mayar da mu wasu yan iska, an manta da cewar kowa dan iskan kan sa ne, mu ne dai da duniya ta san fuskar mu sai a tsane mu” a cewar Ummi Gombe.
A karshe ta ce, “Don haka yanzu an ma wa yan fim bakin fenti, idan mun yi aure sai kawai a rinka ganin an auro yar iska, kuma wannan ba dai-dai ba ne”