Labarai

Babban abin tashin hankalin da yake a rayuwata yanzu shine na mutu ban aurar da ‘ya’yana ba ~ Buhari

Advertisment

Babban abin tashin hankalin da yake a rayuwata yanzu shine na mutu ban aurar da ‘ya’yana ba, domin babu abinda na mallaka a rayuwata wanda in na mutu zan bar gado – In ji Shugaba Buhari
Bayan dawowar sa daga Birnin London na kasar Ingila, a hirar da yayi da ‘yan Jaridu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaidawa ‘yan Jaridun cewa, Babban abin tashin hankalin da yake a rayuwarsa yanzu shine ya mutu bai aurar da ‘ya’yansa ba, domin babu abin da ya mallaka a rayuwarsa eanda in ya mutu zai bar gado illa Gidan Gonarsa guda daya rak.
Kamar yadda opportunities hausa na ruwaito. Shugaban ya ce amma ya zuwa yanzu ya sauke nauyin yaransa da yake kansa, domin idan ya mutu bai aurar da ‘ya’yansa ba ya tabbatar abincin da za su ci sai ya gagare su, saboda babu abinda ya mallaka a Duniyar nan illa Gidan gonarsa kadai, domin shi ba ya sata kuma ba ya bari ayi sata, wannan ce tasa makiya Najeriya suke jin haushinsa.
Buhari ya ce don haka aurar da ‘ya’yanshi ne babban samun kwanciyar hankali a wajensa, domin ya tabbatar ko wacce Mijin ta zai riketa bisa gaskiya da rikon Amana, haka shima dan’sa Yusuf, inji Shugaba Buhari.
Daga Kabiru Ado Muhd

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button