Labarai

Duk Abunda Ke Faruwa Damu Laifin Manyan Arewa Ne – Arewa Media Writers

Advertisment

Ya kamata duk wani Dan Arewa yasan da wannan
1, Manyan ma’aikatan Facebook na Nijeriya kashi 80 duk ‘yan kudancin kasar ne, wannan dalilin yasa ake hade kai dasu a rufe shafukan yan Arewa a kuma hana Verified din Pages din yan Arewa don kada suyi karfi.
2, Duk manyan Jaridun kasar nan da aka yi Verified din Pages dinsu, kashi 95 duk na ‘yan kudancin Nijeriya ne, wannan dalilin yasa Reporting dinsu da ake yi, bazai yiwu a rufe Page din ba.
3, Duk wani aiki da manyan Arewa zasu bawa ‘yan Jaridun Nijeriya kashi 99 duk jaridun kudancin kasar suke bawa, wannan dalilin yasa jaridun kudancin kasar suka yi karfin da bazai yiwu a rufe suba.
4, Yankin Arewa ba tada wata babbar jarida mai karfi da a kayi Verified dinta, domin ta dinga kare mana yankinmu na Arewa, saboda manyanmu basu kishinmu ko kadan, Illah Daily Trust ita kuma bamu san me yake damunta ba.
5, Duk Page din da aka yi Verified din shi a Facebook babu yadda za’a yi Facebook su rufe shi, matukar abunda suka yi bai sabawa abunda mai kamfanin Facebook din yake so ba, amma da wuya kaga anyi Verified din Pages kuma a rufe shi saboda wasu sunyi Reporting.
6, ‘Yan Arewa munyi sakaci na rashin zama ma’aikatan dukkannin kafofin sadarwar zamani da ake shigo dasu Nijeriya, wannan hakan babbar Asara ce a garemu, hakan ya farune sanadiyyar manyanmu na Arewa da basu maida hankali akan yankinmu ba.
Menene Mafita Matukar Ana Son Yankinmu Na Arewa Ya Samu Cigaba Ta Yadda Zamu Yi Karfin Da Babu Wanda Ya Isa Ya Dinga Taba Annabinmu, Addininmu Ya Zauna Lafiya?
1, Dole manyan kasar suyi kokari wajan tura ‘yan Arewa su zama manyan ma’aikatan dukkannin kafofin sadarwar dake cikin Nijeriya, ta yadda za’a dinga damawa dasu.
2, Dole manyan kasar su daina bawa jaridun kudancin kasar nan ayyuka, su dawo amfani dana yankinmu domin a inganta namu Jaridun.
3, Dole manyan kasar, sarakuna, da attajirai su hade kansu su dawo yankin Arewa su Gina matasa tare da taimakon matasan da suke da baiwar kere-kere na fasohohin zamani matukar ana son yankinmu na Arewa ya samu cigaba.
Matukar Shugabanninmu basu yi mana wannan gatan ba, babu wani cigaba da yankinmu zai samu, haka zamu zauna muna gani a yita cin mutuncin Addininmu, da yankinmu ba tare da mun iya tabuka komai ba.
Muna Addu’ar Allah ya tsinewa wanda ya kirkiro Sahara Reporters da wanda yayi fostin din cin mutuncin Annabinmu, da wanda yaji dadin fostin din, da wanda ya bada shawarar a yi fostin din, da duk mai hannu a ciki.
Allah ka kare mana mutuncin Annabinmu, Addininmu, Yankinmu, Mutuncinmu daga dukkannin munafukai, makiya masu son ganin bayanmu. Amin
Daga: Comr Abba Sani Pantami,
National Chairman Of “Arewa Media Writers Association”.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button