Labarai

Shugaba Buhari Ya Aika Da Wakailansa Wajen Neman sanya Ranar Auren Zahra Da Yusuf

Advertisment

Shugaba Buhari Ya Aika Wakilai Domin A Sanya Ranar Auren Ɗansa, Yusuf da ɗiyar Sarkin Bichi, Zahra Nasiru Ado Bayero
Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wakilai domin su haɗu da gidan sarautar jihar Kano a sanya kwanan watan auren ɗansa, Yusuf da Zahra Nasiru Ado Bayero.
Rahotanni sun tseguntawa jaridar DAILY NIGERIAN cewa wakilan da shugaban ƙasar ya aika sun haɗa da gwamnoni, ministoci, darakta janar a fannin tsaro a jihar, Yusuf Bichi.
A yanzu haka wakilan sun dira a Kano a yammacin ranar Asabar tare da goro da sauran abubuwan da ake saka rana.
Sannan wakilan za su gana da wasu daga cikin manyan mutane a iyalan gidan Bayero, Idris Bayero da sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero, a ranar Lahadi.
Zahra Nasiru Bayero a yanzu haka tana karatu a jami’ar United Kingdom a fannin zane-zane, yayin da kuma Yusuf Buhari ya kammala karatun digirinsa a jami’ar Surrey, Guildford a ƙasar Ingila
Daga Mutawakkil Gambo Doko

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button