Labarai

Mutumin da ya kai wa Limamin Ka’aba hari ya ce shi “Mahdi ne”

Advertisment

Mutumin da ya kai wa Limamin Masallacin Ka’aba hari a Juma’a 21 ga watan Mayun 2021 ya ce shi “Mahadi ne”
Hukumomin da ke kula da Masallatai biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain sun ce mutumin ya yi yunƙurin halaka Sheikh Bandar Baleelah ne lokacin da yake gabatar da huɗubar Sallar Juma’a.
Kamar yadda bbchausa na ruwaito,Haramain Sharifain ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata 25 ga watan Mayu cewa, mutumin wanda ɗan ƙasar Saudiyyan ne mai shekara 40, ya yi ikirarin cewa shi Imamu Mahdi ne.
Ya faɗi hakan ne a yayin da ƴan sanda suke tuhumarsa. Sai dai hukumar ba ta yi ƙarin bayani kan matakin da aka ɗauka a kansa ba.
Mutumin ya yi ƙoƙarin aikata wannan aika-aikar ne a yayin da yake sanye da harami a jikinsa.
Imamu Mahadi shi ne wani mutum da wasu Musulmai suka yi imanin cewa zai zo a ƙarshen duniya.
Haramain Sharifain ya wallafa bidiyon a shafukansa na sada zumunsa yadda mutumin ya yi yunƙurin kutsawa ga limamin da kuma yadda jami’an tsaro suka murƙushe shi.
Hukumomin sun ce “mutumin ya tunkari mumbarin limamin ne riƙe da makami a masallacin Ka’aba amma an yi nasarar murƙushe shi.”
Wannan shine bidiyon wanda yayi yunkurin kawai imam sheikh bandar baleelah

 

View this post on Instagram

 

A post shared by Haramain Sharifain (@hsharifain)

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button