Hukumar Efcc Ta Cafke gawurtaccen madamfari mai inksnation


Jami’an hukumar EFCC sun samu nasaran cafke hatsabibin ‘dan damfara Omotade Sparks Amos wanda ya damfari talakawan Nigeria biliyoyin Naira da sunan kamfaninsa na yaudara INKSNATION
Jami’an EFCC sun cafkeshi ne yau a garin Sokoto bayan da hukumar EFCC ta shelanta nemansa ruwa a jallo watannin baya, sai yanzu aka ganoshi a Sokoto
Ina wakilan INKSNATION wadanda sukayi ta zagin Datti Assalafiy tare da cin mutunci fa batanci saboda na ja hankalin ‘yan uwa su guji INSKNATION su karbi kudaden da suka biya don a musu rijista saboda damfara ne?, Alhamdulillah yau gashi gaskiya tayi halinta.

Wadanda suka zageni, suka ci mutuncina, suka min sharri da munafurci na yafe wa kowa, Allah Ya yafe mu gaba daya
Wannan dan iskan madamfari ya cutar da ‘yan uwa talakawa Wallahi, sai da ya bari an shiga kulle a farkon bayyana cutar Coronavirus, abincin da talakawa zasu ci ya gagaresu, sai ya bijiro da INKSNATION ya dinga karbe wa talakawa kudi, musamman mutanen mu na Arewa
Muna fatan Allah Ya wulakantashi, Allah Ya hanashi jin dadin rayuwa mugu kawai azzalumi barawo
