MASHA ALLAH: An Sayo Kayan Auren ‘Yar Talla Mai Sallah (Hotuna)
A karshe dai dani tare da iyayen Hauwa’u da kayayyakin da muka saya musu daga gudunmwwar da bayin Allah suka bayar wanda jimillarsa ya kama dubu dari takwas da arba’in Da bakwai Da Naira dari biyu Da tamanin 847,280.00.
Abubuwan Da muka Saya sune Kamar haka
1.Gado
2.katifa
3.complete set Na kujeru
4.labule(curtain)
5. Ledar tsakar Daki Yadi Goma
6. Kayan kitchen complete
7. Bed sheet
8. Turmi Na daka
9. Food flask, flates, spoons da Sauransu.
10. Buhun shinkafa guda 2 guda 1 Za’a Hada Mata a Cikin kayan Gara, sauran guda 1 Kuma iyayenta Za suyi amfani Da ita a gidansu.
Haka zalika tunda Aure Za’a yiwa Hauwa’u munyi Mata Tanadi Na musamman domin dogaro Da kanta a gidan miji, Mun Saya Mata
1.Keken Dinki
2.Awakai guda 4 Maza 2 Mata 2 Domin kiwo, 3.Sai Naira dubu Hamsin 50,000 (50k) Za’a sayi itace ta dinga siyarwa a gida Duk dai sbd taci gaba Da kulawa Da Kanta.
Itama mahaifiyarta an bata dubu Hamsin (50k) Domin ta Kara jarinta Na sana’ar awara da take Yi.
A bangaren mahaifinta kuwa Shima ya rabauta da Naira dubu Hamsin (50k) domin yaci gaba Da Sana’arsa ta fruits Daya dena yi sakamakon rashin jari. A farko munyi niyyar bashi dubu 100 ne Amman sakamakon Mun fahimchi gidansa Yana bukatar Yan gyare gyare Sai Muka bashi dubu Hamsin ya Kara jarin Sauran dubu Hamsin din Da sauran kudin Daya rage za muyi amfani dasu wajen gyara musu bandaki, Dakin girki, Rijiya Da wani bangare Na katangar jikin gidan data Rushe a gidan nasu Hauwa’u.
Total kudin furnitures, Katifa, ledar tsakar Daki 346,500
Total kudin keken dinki, Awakai, shinkafa buhu 2 labulaye Da Sauransu 210,500
Transport cost 22,000
Mun Chika 43,000 Mun sayi sauran kayan Kitchen sbd akwai wata Baiwar Allah data bamu wasu Daga cikin.
Total kudin Da aka Bawa Hauwa’u Da iyayenta Da sauran 50k Da za’ayi musu gyara ya dubu dari takwas da goma 832,000.00
847,280-822,000 = 25,280.00
Kudin da ya rage 15,280.00 sune zamu Hada Da sauran Dubun Hamsin din Da muka ware domin gyara Wani bangare Na Cikin gidansu Kamar yadda nayi Bayani a Sama.
Mun ja hankalin saurayinta Wanda shine zata Aura Da yayi kokari ya rike Hauwa’u Da Amana Kuma ya Kara tsaya Mata taci gaba Da zuwa makarantar Islamiyyar data Saba zuwa tunda Matan Aure ma suna zuwa.
A karshe Ina jinjina Da godiya ta musamman ga wadanda suka bada gudunmowa ta kudi, wasu Daga cikin kayan kitchen, Shawarwari Da addu’a Allah ya Sakawa Kowa Da Alkhairi, Allah ya biya mana dukkan bukatunmu Na Alkhairi.
Daga Abdulmutallib Hamza Kibiya
02-01-2023.