Labarai

Kotu Ta Ki Amincewa Da Bukatar Kananan Hukumomin Kano Na Hana Gwamnatin jihar Amfani Da Kudadensu

Babbar kotun tarayyar dake Abuja ta ki amincewa da bukatar kananan hukumomin Kano na dakatar da gwamanatin jihar daga amfani da kudadensu wajen gina gadar sama a unguwannin Dan agundi da Tal’udu.

Rahotanni sun ce kananan hukumomin sun shigar da korafin ne ta ofishi shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na jihar Kano ALGON a ranar 27 ga watan disamba,majiyarmu ta ruwaito ta premier Radio kace Kano.

Kotu Ta Ki Amincewa Da Bukatar Kananan Hukumomin Kano Na Hana Gwamnatin jihar Amfani Da Kudadensu
Kotu Ta Ki Amincewa Da Bukatar Kananan Hukumomin Kano Na Hana Gwamnatin jihar Amfani Da Kudadensu

A takardar karar, shugabannin kananan hukumomin sun yi karar gwamnatin Kano ne da kwamishinan shari’a na jiha dama babban akanta na Kano.

Jaridar solacebase ta rawaito cewar Alkalin kotun Mai sharia, Donatus Okorowo ya umarci kowanne bangare da ya bayyana a gabansa a ranar 3 ga watan janairun 2024, inda gwamnatin Kano zatayi bayanin dalilin da zai hana kotun bada umarnin dakatar da aikin.

Sai dai da yammacin Juma’ar nan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya aza harsashin ginin gadojin saman da kasa a shataletalen Tal’udu da Kofar Dan Agundi.

Da yake jawabi yayin aza harsashin ginin gadojin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za a gina su ne domin rage cunkoson ababen a manyan titunan jihar Kano.

Ya kara da cewa bisa al’ada ana gudanar irin wannan tsakanin gwamnatin jiha da kananan hukumomi.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano, Suhaib Auwal Gwagwarwa, ya ruwaito kwamishinan ayyuka na jihar Kano Injiya Marwan Ahmad na cewa za a samar da kananan hanyoyi domin ragewa al’umma wahalhalun zirga-zirga da aikin gadojin zai haifar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button