Labarai

‘Yan Kungiyar IPOB Sun kashe ‘Yan Arewa Fulani Mutum 19 (Hotuna)

Jiya Lahadi da misalin karfe daya na daren yau Litinin ‘yan ta’addan kungiyar IPOB masu ikrarin kafa Kasar Biafra sun shiga gidajen fulani da suke zaune a wani gari da ake kira Igbariam karamar hukumar Oyi jihar Anambra suka hallaka mana ‘yan uwa fulani mutum 19
Cikin ‘yan uwan mu fulani 19 wanda ‘yan ta’addan IPOB suka hallaka akwai mata da yara kanana masu shekaru 2 da shekaru 3
Fulanin basu aikata laifin komai ba aka musu wannan kisa na kare dangi, laifinsu kawai shine don sun kasance ‘yan Arewa suna zaune a yankin Inyamurai
Ya kamata Gwamnatin Nigeria tayi gaggawan daukar mataki tare da zakulo wadanda suka aikata wannan danyen ta’addanci don su fuskanci hukunci, bai kamata a mayar da rayukan ‘yan Arewa kamar na sauro da za’a kashe a banza ba
Muna rokon Allah Ya karbi shahadar su
Allah Ya tona asirin wadanda suka kashe su, Majiyarmu ta samu tattara Wannan labari daga Datti Assalafy

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button