Labarai

Wani fim ‘The kerala Story’ kan matan India da suka shiga kungiyar ‘ta’addanci’ ta Islamic State ya jawo ce-ce-ku-ce

Wani tallafar fim wanda ake ikirari da cewa wata sabuwa kungiyar ta’adda ci ce ta islam wanda ya jawo musanyar yawo ga al’umma da kuma shafukan sada zumunta ga yadda jaridar Bbchausa na ruwaito yadda binciken su ya nuna.

Wani fim kan matan India da suka shiga kungiyar 'ta'addanci' ta Islamic State ya jawo ce-ce-ku-ce
Wani fim kan matan India da suka shiga kungiyar ‘ta’addanci’ ta Islamic State ya jawo ce-ce-ku-ce

Ministan ya aike wa ‘yan sanda bukatar dan jaridar Arvindakshan BR.

“An soma gudanar da bincike. Mun nemi shawarwarin masana shari’a a kan wannan takardar game da hukuncin da ya kamata mu yanke,” a cewar Sparjan Kumar, kwamishinan ‘yan sanda Thiruvananthapuram, babban birnin jihar Kerala.

A cikin tallan fim din, wata mace sanye da hijabi ta ce a baya sunanta Shalini Unnikrishnan kuma ta so ta zama ma’aikaciyar jinya.

“Yanzu sunana Fatima Ba, mamba a kungiyar ta’addanci ta IS da aka kulle a Afghanistan,” in ji ta, tana mai karawa da cewa akwai ‘yan mata “32,000 irin ta da suka zama ‘yan kungiyar kuma an binne su a saharar Syria da Yemen bayan an kashe su”.

“Ana sanya ‘yan matan da ba su ji ba ba su gani ba cikin kungiyar da ke da hatsarin gaske a Kerala,” in ji ta.

Kimanin mutum 440,000 suka kallo tallan fim din a YouTube a kwanaki shida da suka gabata kuma yayin da wasu suka yane shi wasu sun soke shi.

Adah Sharma, tauraruwar fim din, ta wallafa tallan fim din a Tuwita tare da maudu’in #TrueStory. Furodusan fim din, Vipul Shah, bai bayar da amsa kan sakon da BBC ta aika masa ba.

Mr Arvindakshan, dan jaridar, ya shaida wa BBC cewa ya nemi a gudanar da bincike sannan ya bukaci mutanen da suka hada fim din su fitar da shaidu saboda ya fusata game da ikirarin da aka yi a tallan ba.

“Watakila wasu daga cikin abubuwan da aka fada sun faru amma idan aka ce ‘yan matan sun kai 32,000 wannan babban lamari ne,” a cewarsa.

A wata tattaunawa da ya yi da Citti Media a 2021 – kamfanin da ke yada labarai – daraktan fim din ya ce ya samu adadin ‘yan matan da suka shiga kungiyar IS ne daga bayanan da tsohon ministan Kerala Oommen Chandy ya gabatar wa majalisar dokokin jihar.

Mr Sen ya yi ikirarin cewa Mr Chandy ya ce “duk shekara ‘yan mata tsakanin 2,800 zuwa 3,200 ne suke Musulunta” don haka kenan ‘yan mata 32,000 ne suka karbi shahada a shekaru 10.

Sai dai wani bincike da shafin intanet na Alt News da ke bincike don gano gaskiyar labari na India ya ce “babu wata shaida” da ke gaskata ikirarin Mr Sen.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button