Addini

Kasuwancin Cryptocurrency Haramun ne- Bn Usman

Babban limanin masallacin juma’a na Sahaba da ke nan Kano Sheik Muhammad Bin Usman ya ce kasuwanci zamanin na internet (Cryptocurrency) musamman Bitcoin haramun ne da ya kamata jama’a su gujeshi.
Kano Focus ta ruwaito malamin ya bayyana haka ne ya yin karatun daya gabatar mai taken hakkokin musulmi guda shida kamar yadda yake a sahihu Muslim a ranar Lahadi.
Ya ce da yawan mutane suna shiga tsarin bisa ganganci yayin da wasu ke shiga a jahilce.
A cewarsa wanda ake dangantawa da kirkiro tsarin a shekarar 2009 Santoshi Narcomoto ya na barranta kansa dashi.
“Shi kansa yana musanta cewa shi ne ya kirkiro tsarin, to kaga ta fuskar asali ma ana kai kawo kan wanda ya kirkiro shi.
“Wasu kuma suna cewa wani mutum ne dan kasar Australia ya kirkiro shi to kaga yana da kyau duk abinda zaka yi kasan a salin sa tukunna,” a cewar sa.
A don hakan ne ya ja hankalin al’umma da su kauracewa shiga tsarin zuba jari ko kasuwanci ta internet da ake kira da Bitcoin duba da irin hatsarin da yake dashi.
Ya ce a farkon fitowar sa duk Bitcoin yana dai dai da digo daya na senti, wato kudin kasar amurka inda daga bisani yakai guda daya za a baiwa mutum dala talatin da biyar.
“A yanzu kuma Bitcoin daya sai ka bada dalar amurka dubu goma sha daya za a baka guda daya kaga ai ya zama hauka.
“Kuma wannan kudi idan kace za kayi harka dashi idan ka karye ba wanda zaka kama kace ya biya ka, tunda babu wata kasa da ta yarda dashi don haka ba kudi bane,” inji shi.
Ya kuma ce wandanda suka kirkiro da abin sun raina hankalin al’umma ne don haka ya zama wajibi a fadakar.
“Irin wadannan tsare-tsare suna da yawa kamar Mapurodi da ya kirkiro da kamfanin Ponzi scheme an kamashi sau da dama saboda laifin damfara, da irin su malty-level marketing da pyramid,” a cewar sa.
Ya ce malamai sun dade da bata fatawa cewa haramun ne saboda makirci ne da cuwa-cuwa a don haka bai kamata mutane da sunji maganar kudi su rinka cusa kansu ba.
“Arziki idan aka nufeka za ka samu, za ka samu idan ba a rubuta maka ba to ba za ka samu ba saboda haka kada ka wahalar da kanka.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button