Labarai

Babban bakin Najeriya CBN ya ƙara korar wasu ma’aikata 50

A ranar Litinin din da ta gabata ne Babban Bankin Nijeriya, CBN ya kori karin wasu ma’aikata guda 50, lamarin da ya kara yawan ma’aikatan da aka kora, inji rahoton Daily Trust.

Daily Trust ta rawaito cewa korar da aka yi, a karkashin jagorancin gwamnan CBN, Mista Olayemi Cardoso, an yi ta ne a sashe-sashe 29 na bankin.

Ya zuwa yanzu, CBN don ya kori ma’aikata 117 a cikin kwanaki 20 da suka gabata.

Korar ta shafi daraktoci, mataimakan daraktoci, manyan manajoji, da kuma ƙananan ma’aikata.

Ana ci gaba da aika wasikun sallamar wadanda aka fara a ranar 15 ga Maris, duk mako, in da hakan ya jefa fargaba a tsakanin ma’aikatan kowane sashe saboda bankin bai fitar da wani tsari na korar ba, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa wakilin Daily Trust.

Tun da aka fara korar, hikimomi a babban bankin sun ki cewa komai kan lamarin.

Ko a lokutan baya, kokarin jin ta bakin mukaddashiyar Daraktan Sadarwa na CBN, Hakama Sidi Ali, ya ci tira, domin ba ta dauki wayar da jaridar ta buga mata, ko kuma ta mayar da sakon kar-ta-kwana da aka aika a layinta ba.

-Daily Nigerian Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button