Tallafin Covid-19: An gane ba Buhari ne matsalar Najeriya ba (Hoto) – Zahra Buhari
Kwanaki kadan da suka gabata, ‘yan Najeriya sun gano ma’adanar da aka killace kayan abincin tallafin COVID-19 wanda CACOVID suka bayar, kuma sun fada gidajen sun kwashesu tas.
Majiyarmu ta samu daga Legit, Kayan tallafin sun hada da kayan abinci iri-iri wadanda ya kamata a rabawa talakawan Najeriya.
‘Yan Najeriya da dama sun yi ta caccakar gwamnatin jihohi a kan rashin raba kayan abinci da ya kamata su yi lokacin da aka shiga tsanani.
Wata mai shirya fina-finai, Mansurah Isah, ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta nuna yadda aka gano kayan tallafin, wanda hakan ke nuna ba shugaban kasa ne matsalar Najeriya ba.
Zarah Buhari-Indimi, wacce diya ce ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta kara wallafa wallafar Mansurah a shafinta na Instagram, da alamu ta yadda da abinda Mansurah Isah ta wallafa.