Tuhumar Malam Abduljabbar Za A Yi, Ba Mukabala Da Shi Ba– Sheikh Khalil


A cikin tattaunawarsa da LEADERSHIP A YAU a daren jiya, Sheikh Khalil, ya ce, ba mukabala za a shirya tsakanin Malam Abduljabbar da sauran malamai ba, a’a, za a zaunar da shine a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin tsammanin da mutane suka yi tun a baya.
“Ba mukabala ba ce, tuhuma ce. Idan aka kira shi mukabala, an canja masa ma’ana. Abiunda za a yi tuhuma ce. Ba mukabala za a yi da Abduljabbar ba, a’a, magana ce ta tuhuma. Don haka ba mukabala ba ce. Mutane suna da surutu suna cewa, mukabala-mukabala. Ba mukabala ba ce, tuhuma ce.’ inji shugaban malaman.
Ya kara da cewa, “abinda ya sa ya zama mukabala shine, saboda yana yin wasu bayanai kan wadansu hadisai da kuma akan wadansu sahabbai. Bayanin da su malamai suke ganin cewa, akan sahabbai da kuam yadda yake bayani akan wadansu hadisai, to ba haka suke ba. Don haka shi yasa suke tuhumar wadannan bayanai ko maganganu da yake yi akan su sahabbai…
“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi? A malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi? Shi ya sa ya zama tuhuma. Ita kuwa mukabala ita ce, kai kana cewa kaza, wancan yana cewa kaza, to sai a zo a auna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi! Shine za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama daidai?”
Yayin da muka tambaye kan cewa, idan tuhuma ce, to za a yi tsammanin hukunci ya biyo baya kenan, sai ya ce, wannan kuma gwamnati ko kotu ne za su abinda ya dace. Don haka gwamnati za a tambaya, ba Majalisar Malamai ba.
Ya kara da cewa, an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a Kano, amma ba a taba ganin irin fahimtar da Malam Abduljabbar ya zo da ita ba, yana mai cewa, shi kansa mahaifinsa Malam Abduljabbar, wato Marigayi Sheikh Nasiru Kabara, Amirul Jaishi kuma jagoran darikar kadiriyya a Afrika ta Yamma, bai taba hawa irin wannan turbar da dan nasa ya hau ba.


