Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un : Allah ya yi wa sananniyar mai fassara Al-Qur’ani mai girma rasuwa
Valeria (Iman) Porkhova, sananniyar mai fassara Al-Qur’ani da yaren Rasha ta rasu – Ta rasu ne tana da shekaru 79 a duniya – Fassararta kadai ce wacce aka yi da ayoyi kuma manyan malaman musulunci na duniya suka aminta da ita Sananniyar mai fassara Al-Qur’ani da yaren Rasha, Valeria (Iman) Porkhova, ta rasu a Moscow tana da shekaru 79 a duniya.
Kafafen yada labarai na Rasha sun ruwaito cewa ta rasu ne a ranar Litinin, 2 ga watan Satumba. Rahoton ya kara da cewa addu’ar tunawa da ita a ranar Laraba 4 ga watan Satumba a wani masallaci da ke Moscow.
An haifeta a shekarar 1949 a garin Tsarskoye Selo a kasar Rasha. Porokhova ta kammala karatunta a Moscow State Pedagogical Institute of Foreign Languages kuma tayi aikin koyarwa na shekaru 18. Daga baya ta koma aiki a Russian Academy of Natural Sciences.
A shekarar 1975, ta auri wani dan kasar Syria inda suka bar Moscow zuwa Damascus a 1981 inda ta amshi musulunci ta kuma sami sunanta na Iman. A kasar Syria ta fara aikin fassara Al-Qur’ani mai girma zuwa yaren kasar Rasha. Ta kammala fassarar a 1991. Rahoto ya nuna cewa fassararta ita kadai ce wacce aka yi da ayoyi kuma malaman musulunci na kasashe daban-daban da suka hada da jamhuriyar Soviet suka aminta da ita.
Allah Ya Jikanta Da Rahama
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.









