Kannywood
Ana bukatar malamai da al’umma wajen gyaran fina-finai – Aminu Saira


Advertisment
Wani mai shirya fina-finan Hausa a nan Kano Malam Aminu Saira, ya ce, idan har ana son gyara harkokin fina-finai to wajibi ne sai malamai da kuma al’umma sun shigo cikin lamarin domin samun gyaran da ya dace.
Aminu Saira ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Freedom Radio, yana mai cewa yadda mutane suka yi watsi da lamarin fina-finan Hausa ne ya sanya a ke samun matsalolin da ake gani yanzu.
A cewarsa “Da mahukunta su shigo cikin harkokin shirya fina-finai da zuwa yanzu an gyaya duk wata barna da ake ganin ana yi a cikin masana’antar shirya fina-finan ta Kannywood.”

