Masarautar Gumel ta saukakawa Matasa yin Aure:Karanta Jadalin abubuwa 6 kacal da ake bukatar Ango ya samar
Masarautar Gumel ta saukakawa matasa yin aure inda ta haramta sauran abubuwan al’ada da ake yi yayin Bukukuwa.
Bayan Sadaki, Masarautar tace kayan da ake bukata Ango ya kaiwa Amaryarsa kawai sune.
Jerin kayan Kwalliya 2.
-Dankwali 3.
– Hijabai da Mayafai 3.
-Dan Kunne da Sarka 3.
-Takalma 3.
-Da Kayan sawa Kala 6.
Ko dai Zazzau Emirate Council ta yi mana irin wannan dokar ko kuma mu tafi Gumel mu karo aure ?
– Dan atamfarka da leshinka 6
– ‘yan kunni guda 3
– Gele da hijabi 3
– Dan kwali 3
– Su jan baki da gazal da hoda saiti 3 a shafa Fatiha kawai a tashi https://t.co/g3i772ebZ4— Abdallah Yunus Abdallah (@Abdool85) February 17, 2021
Hadimin gwamnan Kaduna, Abdallah Yunus Abdallah ne ya bayyana haka inda yayi kira da cewa ya kamata Sauran Masarautu su yi koyi data Gumel Din dan saukaka Aure.
Yakamata masarautar kazaure tayi koyi da masarautar gumal