Labarai

Za a kashe wata tantabara da ta saɓa dokar killace kai a Australia

Advertisment

Za a kashe wata tantabara da ta ƙetara Tekun Pacific bayan ta karya dokar killace kai ta ƙasar Australia.
A baya dai an bayar da rahoton ɓacewar tantabarar yayin tseren tantabaru a jihar Oregon ta Amurka a watan Oktoba, inda bayan watanni biyu aka ga tantabarar a birnin Melbourne na Australia.
Sai dai jami’ai sun bayyana cewa tantabarar wadda ake wa laƙabi da Joe, na barazanar yaɗa cuta ga tsuntsayen ƙasar.
Kamar yadda BBCHAUSA na ruwaito.Wani mazaunin birnin Melbourne Kevin Celli-Bird, ya bayyana cewa ya ga tantabarar a lambun bayan gidansa a ranar 26 ga watan Disamba.
Ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa ko da ya ga tantabarar, da alamu ta tagayyara, wanda hakan ya sa ya daddaka biscuit ya ba ta.
Ya kuma bayyana cewa bincike da ya zurfafa ta intanet ne ya gano cewa tsuntsun mallakar wani mutum ne a jihar Alabama ta Amurka, kuma an yi wa tantabarar ganin ƙarshe a watan Oktoba
A halin yanzu dai za a kama tantabarar a kashe ta.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button