Fitsararriyar yarinya nan Farakhiyya hashim tayi mummunan kalamai akan auren sarkin daura
Yarinyar ta nuna cewa irin auren ‘yar shekara 17 da sarkin daura yayi to yakamata su fito su yaki akan wannan abu da yayi da bai dace ba.
Ita a nata ganin irin wannan abubuwan na auren wuri shine ke kawo kashe kashe da rashin zama lafiya da ta’addanci da ke faruwa a arewa maso yamma da kudancin Nigeria a nata tunani tayi wannan kalaman ne shafinta na twitter.
Alhamdulillah ɗan babban shehin malami ashe prof Muhammad sani umar R/lemo yayi mata martani mai hikima cikin ilimi da nunawa duniya ko wacece ita a al’ummarmu ga abinda yake cewa.
“A yayin da duk duniyar mutane masu hankali kowa ya san cewa irin matsalolin da muke fama da su ba komai bane suka haddasa su ba face zalunci da jahalici da rashin ayyukan yi da yawaitar rashawa da kuma rashin kyakkyawan shugabanci magance waɗannan shi zai kawo mana sauƙi ita kuwa “Sherlock Holmes” ɗin arewa garkuwar tsaron duniya wayayyiya (enlightened) ƴar wayayyu ra’ayinta shi ne duk wannan halin da muke ciki shine auren wuri da ƴan arewa suke yi !! Da zarar kuma sun daina aikata hakan to nan duk wannan masifar zata kau wataƙilama mu zama tamkar Switzerland !!
Irin wannan tunanin shine tunanin duk ƴan boko aƙidar da suke cikin musulmai suke ɗauke da shi yayin da masu hankali suka yi ittafaƙi akan abubuwan da suke kawo mana koma baya da kuma abubuwan da yakamata a yi don warwaresu sukuwa gani suke auren wuri da littafan ibnu Taimiyyah da Bukhari da sauran littafan malaman musulunci sune musabbabin komai ba za a samu zaman lafiya ba sai an watsar da su!!
Allah mungodema bisa ni’imar hankali“