Labarai

Shagalin Bukin Diyar Ganduje : Tashin Hankali ne Da Tabarbarewar Tarbiyya Ga ƴa ƴanmu Mata Inji Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi

⏩ Dakta Ahmad Gumi, yayi Allah wadai da irin badalar da aka yi a bukin diyar gwamnan jihar Kano

⏩ Dakta Ahmed Gumi ya soki hukumar Hisba jihar Kano akan rashin daukan mataki saboda badalar da aka yi a bukin diyar Ganduje

⏩ Dan gidan marigayi, Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Dakta Ahmad Gumi, yayi Allah wadai da irin badalar da aka yi a bukin diyar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje.

Dakta Ahmed Gumi, ya ce har idan kanawa basu shiga taitayin su ba, azabar Allah zai iya fado musu ta sanadiyar haka saboda yin haka tashin hankali ga addinin musulunci.

Shehin Mallamin, ya bayyan haka ne karatun Dandalin Sunna da ya saba yi a kwani mako a masalacin Sultan Bello.”Ku duba irin abin da akayi a Kano, Abin yana bani bakin ciki. ace diyar gwamnan ta fito tana rungumar wani kato. Sannan kuma a garinne aka dakatar da wata ‘yar fim don ta rungume namiji. Toh ga diyar gwamnan ku ta runguma kenan yanzu za a halatta barin haka ya cigaba da faruwa zai lalata tarbiyar yaran mu.

”Sannan ina hukumr hisbah suke, shugabannin da muke sa wa kenan. Wallahi kunga yadda Allah ya maida garuruwa, to wallahi garin Kano suyi hankali, da wannan fasikancin Allah zai iya halaka garin Kano. Kunga yadda Maiduguri ta zama ,” Inji shi

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button