Uncategorized

Biki Bidiri : An ɗaura auren matashi ɗan Kano da Ba’amurkiya (Bidiyo Da Hotuna)

Hausawa kance rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, yau Lahadi ne aka ɗaura auren matashin nan ɗan jihar Kano wato Isa Sulaiman Panshekara mai shekara 26 da sahibarsa Ba’amurkiya.

Ama

Ɗumbin mutane ne suka taru a masallacin Jumma’a na Gasau dake ƙaramar hukumar Kumbotso, domin shaida ɗaurin auren da aka jima ana dako, bayan shafe tsawon lokaci suna shan soyayya.
Matashin ya biya zunzurutun kuɗi har Naira Dubu 50 a matsayin sadaki lakadan ba ajalan ba.
Amarsu ta ango

Mahaifin ango Mallam Sulaiman, ya shaidawa BBC cewa ya amince a ɗaura auren ne bayan amincewa da dukkanin sharuɗɗan da ya gindaya kafin ya bayar da ɗansa.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarci ɗaurin auren har da Sanata Shehu Sani, tsohon Sanata mai wakilar jihar Kaduna a majalisar dattawa ta tarayyar Najeriya, da kuma shugaban ƙaramar hukumar ta Kumbotso.
Abin jira a gani shine lokacin da Ango zai bi Amarya, duba da cewa jim kaɗan bayan ɗaura aure uban ango ya ce ɗansa zai ci gaba da zama da shi, sai dai kuma shi angon ya ce za a jira ne zuwa lokacin da za a kammala tattara takardu.
Ga bidiyon daurin auren suleman da baturiya kenan wanda Freedom radio kano na kawo kai tsaye.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button