Uncategorized

ADDU’AR ZIYARAR MAKABARTA | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*ADDU’AR  ZIYARAR MAKABARTA*

*Tambaya:*
SLM Malam wacce addua’a mamaci yafi bukata ? ko kuma Idan an ziyarci kabarin sa wacce addu’a za’a masa ?
*Amsa:*
Wa alaikum as salam, Annabi saw ya shar’anta ziyarar makabarta saboda tana tuna lahira, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 3237, kuma Albani ya inganta shi.
In mutum ya je kabari an shar’anta ya fadi wannan adduar :
السلام عليكم أهل الديار من المؤمنين  والمسلمين، وإنا إن شاء الله  للاحقون، أسأل الله لنا ولكم العافية.
Assalamu alaikum Ahlad diyaar minal Mu’umineena wal Muslimeena, wa innaa insha Allahu La laahiquuna, as’alullaha lanaa wa lakumul ‘aafiyah, Muslim a hadisi mai lamba ta : 2302.
Allah ne mafi sani
04/11/2015
*Amsawa*
Dr. jamilu yusuf zarewa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA