Cutar Da Ke Addabar Al’aurar Mata Da Shawarwarin Magance Ta
Wannan wata cuta ce da mafi yawancin jama’a suna kiran ta da suna cutar da ke addabar alaura, masana kiwon lafiya suna kiran ta da cutar da ke addabar alaurar mata, saboda wannan cuta tana addabar gaban mace. Amma a Hausance ana kiran ta da ciwon sanyin mata.
Wannan cutar dai wasu kwayoyin cuta ne masu illatarwa. Babban mutum zai iya kamuwa da shi, haka ma yara za su iya kamuwa da wannan cutar. Ba wai kawai ta hanyar jima’i ake daukar wannan cut aba, ga kadan daga cikin hanyoyin kamuwa da cutar kamar haka:
Amfani da kayan aiki ba tare da an tsaftace su ba lokocin haihuwa ko wanke jiki.
Tsaftace gaba ta hanyar amfani da sabulu mai kashe kwayoyin cuta.
Cusa hannu ko yatsa a gaba.
Amfani da wandon wata musamman fant.
Barin wadon (fant) ya dauki datti.
Rashin canza audugan mata akai-akai lokocin al’ada.
Ga kadan daga cikin kwayoyin cutar da suke kawo wannan matsalar kamar haka:
kwayar cutar baginosis: Wannan wani kwayar cuta ce da ke rayuwa cikin farji, ta kan haddasa matsalar sanyin mata.
Candidiasis: Wannan wasu kwayoyin cuta ne wadand suke haddasa sanyin Gaba. Wadannan kwayoyin cuta suna zama cikin farji kuma ba su cika cutarwa ba. Wadannan kwayoyin cuta suna son waje mai gumi domin su girma da yaduwa.
Trichomonas baginalis: Wannan ita ce wacce take yaduwa ta hanyar jima’i. Ita wannan kwayar cutar da ake kira parasite take kawo shi.
Irritation baginitis: Ita wannan cuta ana kiran ta da suna Allergic, wasu abubuwan ne da jikin mutum ba ya dauke ka, ana samun sa wajen amfani da abubuwa kamar irin su kwaroron roba da sabulu ko maganin shafawa.
Alamomin cutar dai sun hada da:
Kumburin gaba.
Canza launin gaba zuwa ja.
kaikayin gaba.
Warin gaba.
kurajen gaba.
Zubar da farin ruwa a gaba.
Jin zafi lokocin Jima’i.
Zafin fitsari.
Abubuwan da mace za ta yi wajen kare kanta daga wannan cuta:
Ka da a tsaftace gaba da sabulai masu kashe kwayoyin cuta: A cikin farji akwai wasu kwayoyin cuta wadanda ba sa cutarwa kuma suna da amfani. Amfaninsu dai shi ne, suna taimakawa wajen ba da kariya ga farji, sai ka ga wasu matan sukan wanke farji da sabulun detol haka, wadannan abubuwan da ake amfani wajen wanke farji yakan kashe cututtuka masu amfani na farji sai masu cutarwa su samu daman shiga. A kiyaye wanke farji da Sabulu da kuma wadansu abubuwa wanda ba mu san kansu ba.
A tsaftace wanduna: Amfani da wandon fant, wasu matan sukan bar wandonsu ya yi datti. Barin datti ko amfani da fant masu datti yakan bai wa kwayoyin cuta daman shiga farji.
Wajen wanke bahaya, mafi yawa mata sukan dauki kwayar cutar da take dubura zuwa farji, wanda ba sa yi wa dubura illa amma sukan yi wa farji illa. Shawara a nan dai shi ne, a fara wanke farji kafin a wanke dubura.
Amfani da fant na wasu: Zai iya yi wa wacce kuke amfani da fant daya tana da cutar sanyi. Idan kin yi amfani da nata ke ma za ki iya dauka sai a kiyaye.
Mutum yakan iya daukan wannan cutar lokocin saduwa da namiji idan namijin yana dauke da shi. Hanayar kariya ita ce, amfani da kwaroron roba lokocin saduwa.
A kiyaye amfani da magungunan gargaji musamman wanda ake cusa su a gaba, suna taimakawa wajen samun kwayoyin cuta.
Me ya sa korafin rashin warkewa ya yi yawa?
Idan namiji da matarsa suna dauke da wannan cutar, abin da ya dace dukkansu biyu za su fara shan magani bawai matar kadai ba, muddin daya daga cikinsu ne yake shan magani to akwai matsala.
Duk matar da aka daurata a kan magani, duk sanda ta cire wandonta ya kamata ta wanke da sinadarin da ke kasha kwayoyin cuta kafin ta maido wandon, hakan yana taimakawa wajen warkewa.
Idan aka ci gaba da shan magani kuma ba a kiyaye wasu hanyoyin da suke kawo wannan cutar ba, shi ma akwai matsala sosai.
Shawara:
– Bayan an je asibiti an bada magani, bincike ya nuna tsarki da ruwan dumi da dan gishiri yana rage kaikayi kuma yana kashe kwayar cutar.
– Haka kuma man kwakwa yana kashe kwayar cutar fungal.
-Lokocin da aka dauraku kan magani, ya kamata a kauracewa jima’i gabaki daya ko kuma a yi amfani da kwaroron roba.
Allah Ubangiji Ya ba mu Lafiya.
Jaridar leadershipayau na wallafa wannan rubutu.