Uncategorized

Yadda Za Ki Kauce Wa Da-na-sani A Matsayinki Ta ‘Ya Mace

Advertisment

A matsayinki na ‘ya mace wacce ta fara mallakar hankalin kanta, mahaifiyarki ce ta fi kusanci da ke. Kuma ita ce wacce ya kamata ki rika shawarta a dukkanin lamuranki maimakon kawaye ko saurayi. Duk da cewa babu laifi wajen neman shawarar kawayen da kuma saurayi, to amma abin da ya sa a kullum nake kalubalantar wannan dabi’a ta maida kawa ko saurayi abokin shawara ba komai ba ne illa irin yadda wasu ‘yan matan kan jinginar da mahaifiya a lamuransu, wanda hakan ina ga kuskure ne babba ba karami ba. A matsayinki na uwa wani abin ke ce kawai za ki dauki haske ki shiga lamuran ‘yarki ko da ba ta sanar da ke ba.
Wasu iyayen sun dauka kawai su yarinya ta ci ta sha, a kora ta islamiyya ya wadatar ba ta bukatar wani dan taro ko sisi domin biyan wasu bukatunta na musamman. Dan’uwana kanwarka ko yayarka in ka ji da dan canji a aljihunka daure ka dan ba ta wani abu. Wata ma tambayarka za ta yi, to dan Allah a rika daurewa ana ba su lokaci zuwa lokaci ko dan gudun ka da ta rika tambayar saurayinta. Dan kayan kwalliyar nan a rika daurewa ana siya wa kanne. Wallahi wata kayan kwalliyar ma ta dogara ga saurayi ne, idan kanwarka ta zama haka komai na iya faruwa. Ka riga ka san halinmu samarin zamani.
Abin zai ba ka mamaki ka ji yarinya na tambayar saurayinta wani dan adadin kudi wanda bai taka kara ya karya ba. Illar da ke tattare da tambayar saurayi kudi Allah ka dai ya san iyakarta, domin tana daga cikin hanyoyin da ke haifar da alakar banza a tsakanin masoya.
 
Ba yadda za a yi wani saurayin ya dau kudi ya ba ki ba tare da ya taba jikin ki ba, idan ma bai fara taba ki a farko ba, idan tafiya ta yi nisa yana iya zuwa miki da wannan mummunar bukatar. Yana da kyau idan ki na da wata ‘yar bukata ta kudi ki tambayi mahaifiyarki ko mahaifinki ko yayanki maimakon saurayi.
Abin zai ba ka mamaki matuka yadda ‘yan mata da yawa ba sa rufe sirrinsu ga samarinsu, duk halin da suke ciki ko yanayin da suke suna iya sanar da samarinsu. Idan kika yi abu da saurayinki kwata-kwata ki daina tunanin sirri kuka yi. Wani da zarar ya bar wajen ki ko makwancinsa ba zai nufa ba, har sai ya nemi wani ko wasu daga cikin abokanansa ya sanar musu.
Duk saurayin da zai taba jikinki ko kuma ya nemi yin lalata da ke wai kuma ya budi baki ya ce miki wai saboda tsabar son da yake miki ne ya sa, to karya yake yi da zarar ya biya bukatarsa ba shashasha irinki a wajensa, kuma yana iya rabuwa da ke a kowane lokaci. Kamar yadda ba za ka so wani ya lalata kanwarka da sunan yana son ta ba, to kai ma kada ka lalata kanwar wani wai da sunan kana sonta karya kake.
Ki tsoraci saurayi mai hirar banza idan kuna a tare ko kuma in kuna waya da shi. Idan kina son shi da gasken-gaske yi kokari ki ga ya daina, idan kuma bai daina ba ki yi maza ki hanzarta cire shi a zuciyarki tun kafin ya fara aikata irin abubuwan da bakinsa ke fada. Wani sa’in ‘yan mata ina ga laifinku ne domin kuwa duk lalacewar mutum ina ga sai kin amince zai taba jikinki. Idan saurayinki munanan halayensa suka bayyana kada ki biye masa. Duk yadda za a yi danne zuciyarki kada ki biye masa, in ta kama da rabuwarma ku rabu, in sha Allahu Allah zai kawo miki wanda ya fi shi. In kuma kike ga cewa ba za ki iya rabuwa da shi ba kika biye masa to karshenki dai nadama domin shi abu ne mai sauki ya guje miki da zarar bukatar sa ta biya.
Jaridar leadershipayau ce na wallafa wannan rubutu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button