Labarai

#EndSARS: Ku daina kashe masu zanga zanga~ Hillary Clinton

 
Tsohuwar ƴar takarar shugabancin ƙasar Amurka Hillary Clinton ta yi ƙira ga shugaba Muhammadu Buhari da rundinar Sojoji da su daina kashe masu zanga zanga a jihar Lagos.
Clinton ta bayyana haka ne a sakon da ta walafa a shafinta na Twitter a cikin wannan dare biyo bayan jami’an tsaro da suka farwa masu zanga zanga a Lekki Tall gate da suka yi kunnen ƙashi da umarnin gwamnati na kafa dokar ta baci.
“Ina ƙira ga Muhammadu Buhari da rundinar Soji da su daina kashe matasa dake zanga zangar EndSars”.
Sai dai tuni ta fara shan zafafan martani daga wasu ƴan Najeriya inda wasu dag cikin su ke cewa, “ina take a lokacin da masu zanga zangar ke ƙona dukiyoyin al’umma da gwamnati har ma da kashe jami’an tsaro a jihar Lagos”.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button