Labarai

Ba Zan Goyi Bayan Buhari Ba Idan Atiku Ya Fito Takara- Ministar Buhari Aisha Alhassan

Ministar Harkokin Mata, Aishatu Alhassan ta fito fili ta nuna cewa idan har Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar Ya fito takara a 2019, ba za ta marawa Shugaba Buhari baya in har shi ma ya tsaya takara.

Da take raddi kan bidiyon da ake yayatawa inda aka nuno ministar tana yi masa kamfen, Aisha Alhassan ta nuna cewa Atiku Abubakar Uban gidanta ne tun tana aikin gwamnati kafin ma ta fara siyasa.

Ministar ta ce, ita ba ta siyasar munafunci don haka ba ta tsoron shugaban kasar ya kore ta daga aiki saboda ta yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar addu’ar zama shugaban kasa a 2019.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button