Labarai
Ƙungiyar IPMAN ta mayar da farashin man fetur 162 a Najeriya
Advertisment
Kungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu ta kasa IPMAN, ta umarci ‘ya’yanta su kara kudin farashin mai zuwa Naira 162 kan kowace lita.
Ipman ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon karin kudin mai da gwamantin Najeriya ta yi zuwa N151.56k.
Wata sanarwa da reshen kungiyar na shiyyar kudu masu yamma ya fitar ta ce ba su da wani zabi illa su kara kudin man domin gudun kada su yi asara kamar yadda bbchausa na ruwaito
Shugaban kungiyar ta Ipman reshen Kano mai kula da wasu jihohin arewacin Najeriya Alhaji Bashr Dan Malam ya ce dole ne su yi karin, domin cike fansshe karin da za su samu daga wajen da suke sayo man fetur din sakamakon matakin gwamnati na mayar da fetur din N151.56k.
Wannan ne karo na uku da gwamnati take sauya farashin mai a ‘yan watannin baya-bayan nan, sai dai sabanin wasu lokutan da ake rage farashin, karin na man na wannan karon shi ne mafi yawa a baya-bayan nan.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com



