Kara Girman Nono Da Baya Na Kai Ga Yin Ajalin Mace – Likita
Wani kwararren Likita wanda yake yin aikin fida mai suna Red Dafiewhare ya yi kira ga mata da su nisanta kansu daga kara girman Nono da kuma Duwawu ta hanyar yin fida, inda yake cewar yin haka na iya yin ajalin mutum.
Dafiewhare ya yi wannan kira ne lokacin da yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a Abuja a cikin makon da ya gabata.
Ya ce mata da dama musamman a wannan zamani da muke ciki kan so su sauya wani sashe na jikin su, kamar kara girman Nono ko kuma Duwawunsu. Sau da yawa mata da ke yin haka kan rasa rayukansu.
Akan fada cikin matsaloli kamar su zubar jini,daskarewan jini,yawan kashe,bugawar zuciya da dai sauran su.
Ya kara cewar domin guje wa irin haka ne likitan ya yi kira ga mata da su guje ma yin haka.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne wasu likitoci suka gargadi mata da su guje ma kara girman Nonon su ta hanyar fida saboda matsaloli da akan fada.
Likitocin sun kuma kara da cewa duk macen da ta yi irin wannan fi
da a Nonon ta kan yi fama da matsaloli da suka hada da rashin iya shayar da da nono,kamuwa da cutar dajin dake kama Nono da jini, Nonon da aka kara wa mace kan fashe, ga kuma rashin samun isasshen barci, yawan ciwon kai da baya da dai, sauran su.