Labarai
Banga Amfanin sarautar Kano ba, kamata yayi kawai a mayar da Masarautar gidan Yawon Bude Ido ~Fakhrriyya Wadda Tayi Tir Da Hukuncin wanda Ya zagi Annabi A kashe shi
Advertisment
Tauraruwar me ikirarin kare hakkin bil’adama da hakkin mata, Fakhrriyya Hashim wadda a kwanakin baya ta jawo cece-kuce sosai bayan da ta yi Allah wadai da hukuncin kisan da aka yankewa wanda yawa fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) kalaman batanci a Kano, a wannan karin tace bata ga amfanin Masarautar Kano a yanzu ba.
A wani sako data fitar ta shafinta na Twitter tace a yanzu bata ga amfanin masarautar Kano ba. Tace gara a baya lokacin tsohon Sarki, Muhammadu Sanusi II ya kawo ci gaba a masarautar.
Advertisment
Ta kara da acewa amma Sarkin Yanzu babu alamar zai kawo wani ci gaba inda ta bada shawarar kawai a mayar da masarautar ta Kano wajan yawon bude ido dan a rika samun kudin shiga daga ita.
Ta kara da cewa in banda sarakunan yankin Arewa maso gabas dake shiga sulhu tsakanin wasu rikice-rikice na al’umma, sauran sarakunan duk babu abinda suke yi sun zama sai yanda ‘yan siyasa suka yi dasu tattara wannan bayyani ya fito daga jaridar hutudole.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com