Arewa : Bakar Fata Wanda ya kirkiro “Programming Language”
Wannan shi ne bakar fata dan Nigeria, dan asalin garin Gujba da ke jihar Yobe wanda ya kirkiro programming language da kansa mai suna EasyByte, sunansa Muhammad Baba Goni.
Akwai programming languages kala-kala a duniya, kuma kowanne da aikinsa wadanda fararen fata ne muka sani suke kirkirowa. Amma a yau an samu wani bakar fata dan Nigeria wanda ya kirkiro nashi programming language din.
—James Gosling shi ne ya kirkiro Java programming language
—Bjarne Stroustrup shi ya kirkiro C++
—Rasmus Lerdorf shi ya kawo PHP
—Guido van Rossum shi ya kawo Python
—Muhammad Baba Goni shi ya kirkiro EasyByte
Muhammad wanda aka fi sani da Royalmaster kwararren masanin computer ne. Ya karanci Computer Science a Federal Polytechnic Damaturu inda ya gama da Distinction, sannan ya zarce Yobe State University nan ma ya kammala Degree dinsa a Computer Science da First Class.
Ya kirkiro manhajoji kala-kala kafin wannan lokacin. A yanzu shi Software Engineer ne kuma Blockchain Developer, yana zaune a garin Damaturu da ke jihar Yobe. Na hadu da shi a wannan sahar shekaru goma da suka gabata.
Rubutawa Muhammad Auwal Ahmad mamalakin Founder/CEO, Flowdiary